Rikicin Jam'iyyar APC: Bani da hannu a tsige Kakakin Majalisa, Lalong ya maida martani

Rikicin Jam'iyyar APC: Bani da hannu a tsige Kakakin Majalisa, Lalong ya maida martani

  • Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yi ƙarin haske kan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana da hannu a tsige kakakin majalisa
  • Gwamnan yace ɓangaren majlisa zaman kansa yake, kuma suna tafiyar da harkokinsu ba tare da jiran umarnin wani ba
  • A cewarsa ya taba fuskantar irin wannan lokacin yana kakaki, dan haka ba shi da hannu a lamarin

Plateau - Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya musanta duk wani zargi da ake cewa yana ɗa hannu a lamarin tsige tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Filato raanr Alhamis da ta gabata.

Lalong ya yi wanna furuci ne domin kore duk wata jita-jita da take yawo a kafafen sada zumunta cewa shine ya sa aka tsige kakakin majalisan.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu na ƙarin haske da gwamnatin Fitato ta fitar a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali zan nemi kujerar shugaban ƙasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

Gwamna Lalong
Rikicin Jam'iyyar APC: Bani da hannu a tsige Kakakin Majalisa, Lalong ya maida martani Hoto: @Governor Simong Lalong
Asali: Facebook

Hakazalika gwamna Lalong ya maida martani kan furucin malamin addinin kirista na Jos, Isa El-Buba, a wurin taron godiya na shekara-shekara.

El-Buba ya ƙalubalanci gwmana Lalong da ya dawo da zaman lafiya a majalisar dokokin bayan tsige shugaban majalisan.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa mambobin majalisar sun maye gurbin Honorabul Abok, da Honorabul YaKubu Sanda a matsayin shugaba.

Wane martani gwamna Lalong ya yi?

Gwamnan Filato yace:

"Majalisar dokoki wuri ne dake zaman kansa, waɗan da suke tafiyar da harkokinsu ba tare da dogara da wani ba."
"Kasancewar na rike muƙamin shugaban majalisa kuma aka tsige ni, bani da hannu kan yadda suke tafiyar da harkokin su."
"Ban yi maganar su canza jagoranci ba, suna gudanar da lamurransu ne yanda suke so, kuma ta hanyar bin dokoki da ƙa'idoji."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

Ku daina yaɗa abinda ba tabbas - Lalong

Gwamnan ya shawarci al'ummar jihar Filato, musamman shugabanni su rinka tabbatar da magana kafin su ɗauki ɓangare.

Ya kuma shawarci duk masu tantama akan maganar sa da su tuntubi majalisar domin samun cikakken bayani.

Daga ƙarshe kuma Lalong ya yi kira ga mutane su saka shugabannin su dake kan madafun iko a cikin addu'o'insu.

A wani labarin kuma Tsohon shugabn majalisar dattijai yace ko wane mataki PDP ta yanke zai nemi takarar shugaban ƙasa a 2023

Sanata Anyim, wanda ya fito daga yankin Kudu maso gabashin Najeriya, yace lokaci ya yi da zai fito ya bayyana shirinsa na neman lamba ɗaya a ƙasar nan.

Yace taron da PDP ta gudanar kamar an sabunta tafiyar ne, kuma alama ce ta fara harkokin siyasa gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel