Da Duminsa: Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokokin Filato ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

Da Duminsa: Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokokin Filato ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

  • Rahotanni daga wurin zanga-zangar lumana da matasa ke yi a majalisar dokokin Filato sun ce lamarin ya ɗauki wani sabon salo
  • A halin yanzun wasu matasa da ake tsammanin magoya bayan sabon kakakin majalisa ne, Yakubu Sanda, sun kutsa kai cikin zauren ta kofar baya
  • Hakan ya harzuƙa magoya bayan tsohon kakaki, amma jami'an tsaro suka fara harbi a iska domin kwantar da tarzomar

Plateau - Zanga-zangar lumana da matasa ke yi a kofar shiga zauren majalisar dokokin jihar Filato ya ɗauki wani sabon salo.

Vangaurd tace matasa daga kowane ɓangare na kakakin majalisa, Yakubu Sanda, da kuma wanda aka tsige, Abok Ayuba, sun fara rikici a tsakaninsu.

Matasan dake nuna goyon bayansu ga tsohon kakakin, Honorabul Abok, suna riƙe da allunan rubutu kuma suna rawa a kusa da kofar shiga zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

Majalisar dokoki
Da Duminsa: Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokoki Filato ta dauki sabon salo, An fara harebe-harbe
Asali: UGC

Amma da misalin ƙarfe 8:30 na safe, wasu tawagar matasan suka samu damar shiga harabar majalisar ta ƙofar baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya kawo ƙarar harbin bindiga?

Wasu daga cikin matasan sai da suka farfasa gilasan kofar shiga, har suka isa zauren majalisar inda tsohon kakakin da mambobin dake mara masa baya suke tattaunawa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Yayin da matasan dake waje suka fahimci abinda ke faruwa a cikin harabar zauren, wanda magoya bayan Yakubu Sanda ke yi, sai suka fara hargowar neman ɓalle kofar shiga majalisar inda jami'an tsaro suke.

Hakan ne yasa wasu daga cikin jami'ai suka fara harba bindiga sama domin tsorata mutanen su watse.

Amma matasan sun sake tattaruwa bayan da farko sun yi gudun tsira, sannan suka cigaba da rera wakoki suna masu ɗaga allon rubutu.

A halin yanzun ƙarar harbe-harbe ya lafa, amma matasan na nan a wajen kofar shiga zauren majalisar suna cigaba da zanga-zangan su.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

Yan bindiga sun kai sabon hari Kaduna

A wani labarin kuma kun ji cewa Yan bindiga sun zagaye wurin Ibada, sun buɗe wa mutane wuta a jihar Kaduna

Rahoto ya bayyana cewa yan bindigan sun harbe mutum 2 har lahira yayin da mutane ke tsaka da gudanar da ibadun su.

Hakanan kuma maharan sun yi awon gaba da wani adadi da ba'a gano ba har yanzun zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel