Baba-Ahmed ya bayyana irin dan takara da yankin da arewa za ta goyi baya a 2023

Baba-Ahmed ya bayyana irin dan takara da yankin da arewa za ta goyi baya a 2023

  • Mai magana da yawun NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce 'yan arewa za su zabi dan takara mai nagarta kuma daga kowanne yanki a 2023
  • A cewar dattijon arewan, arewacin Najeriya ba za ta tsorata da barazanar rabewa ba balle ta zabi shugabanta na gaba saboda banbancin addini
  • Ya ce Najeriya ta na bukatar mutum mai nagarta ne kuma wanda zai iya shawo kan matsalolin da suka addabe ta

Kaduna - Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, NEF, ya ce arewacin Najeriya za ta zabi dan takara mai nagarta ne daga kowanne yanki a 2023.

Baba-Ahmed ya ce arewa ba za ta lamunci ko saurari dan takarar da aka fitar ta hanyar bangaranci ko addini ba, TheCable ta wallafa.

Baba-Ahmed ya bayyana irin dan takara da yankin da arewa za ta goyi baya a 2023
Baba-Ahmed ya bayyana irin dan takara da yankin da arewa za ta goyi baya a 2023. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

A yayin tattaunawa da Daily Sun, ya ce halin da kasar nan ke ciki a yanzu ba a bukatar shugaban da za a samar ta hanyar bangaranci ko kuma saboda barazanar rabewar kasar nan.

Read also

Shekaru na 70, amma ba'a taba mumunar gwamnati irin ta Shugaba Buhari ba, Atiku

Ya ce duk wani yunkurin mamaye ofishin shugaban kasar nan ta hanyar tarzoma na iya kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasar nan.

"Ba mu son shugaban kasa ya bayyana ta hanyar kabilanci ko banbancin addini. Ba mu bukatar shugaban kasan da zai iya kulawa da wani bangare na Najeriya kadai. Ba za mu lamunci hakan ba," yace.
"Ya dace ne ya bayyana bayan yin ingantaccen zabe daga kowanne bangare na kasar nan kuma ya kasance shugaban kasa ga dukkan Najeriya. Yankin arewaci za su goyi bayan dan takara daga kowanne yanki wanda ya san matsalolinmu kuma ya ke da karfin ikon shawo kan matsalolinmu."

Ahmed ya ce arewa ta damu da yadda rashin tsaron kudancin kasar nan ke ta'azzara kamar yadda ya ke a sassan arewaci.

Read also

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Ya ce, arewa sam ba za ta girgiza da wasu barazanar rabewa a kasar nan ba kafin zabe mai zuwa kuma ya yi kira ga 'yan awaren IPOB da su daina tada tarzoma a yankin.

"Ba mu son shiryayyen tashin-tashina ko barazana ta samar da shugaban kasar Najeriya. Rabe kasar nan ba zai yi kyau ga kudu maso gabas ba. Ba haka kasar ke so ba kuma babu mai son hakan," yace.

To ka ji: Kungiyar Dattawan Arewa ta bada sharadin goyon bayan ‘Dan Kudu a zaben 2023

A wani labari na daban, Kungiyar dattawan Arewa ta yi bayani game da abin da zai sa ta goyi bayan mutumin kudu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Mai magana da yawun bakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce dole ne a ba su hujjoji masu gamsarwa kafin su mara wa ‘dan takaran kudu baya.

Read also

Zargin komawa APC: Jonathan bai halarci taron gangamin PDP ba, ya cilla kasar waje

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.

Source: Legit.ng

Online view pixel