To ka ji: Kungiyar Dattawan Arewa ta bada sharadin goyon bayan ‘Dan Kudu a zaben 2023

To ka ji: Kungiyar Dattawan Arewa ta bada sharadin goyon bayan ‘Dan Kudu a zaben 2023

  • Kungiyar Dattawan Arewa ta yi karin haske a kan maida mulki ga ‘Yan Kudu
  • Kakakin NEF ya ce sai an gamsar da Arewa kafin ta marawa Kudu baya a 2023
  • Hakeem Baba-Ahmed ya ce tun da siyasa ake yi, ba za ayi wa al’umma dole ba

Kungiyar dattawan Arewa ta yi bayani game da abin da zai sa ta goyi bayan mutumin kudu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Mai magana da yawun bakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce dole ne a ba su hujjoji masu gamsarwa kafin su mara wa ‘dan takaran kudu baya.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.

KU KARANTA: Hon. Kwewum ya rubuta budaddiyar wasika, ya ce PDP ta gaza

NEF ta maidawa Gwamnonin Kudu martani

Baba-Ahmed ya na maida martani game da matsayar da gwamnonin kudancin Najeriya su ka dauka bayan wani taro da su ka yi a Legas a farkon makon nan.

“Dole mutanen yankin kudu su gamsar da ‘Yan Arewa game da abin da za su samu idan mulki ya koma kudu.”
“Idan ka karanta matsayar da su ka fitar, za a fahimci suna son mutumin kudu ya zama shugaban kasa. Hakan ya na nufin arewa za ta sallama kujerar shugaban kasa zuwa kudancin kasar nan. Wannan babu wani laifi.”
“Matsalar ita ce wadanda su ke wannan magana sun samu mulki ne ta sanadiyyar kundin tsarin mulki, wadanda su ka san a siyasa, ana jawo hankalin mutane ne, ba kurum a zauna ana cewa ‘ga yadda mu ke so ba’, wannan ba daidai ba ne.”
To ka ji: Kungiyar Dattawan Arewa ta bada sharadin goyon bayan ‘Dan Kudu a zaben 2023
Gwamnonin Kudu a Legas Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwankwaso bai lissafin ya koma APC inji Hadiminsa

“Na biyu dole su sani cewa salon da su ka bi wajen cin ma wannan manufa zai iya kawo matsala, a maimakon ya shawo kansu.”
“Sai an nuna mana meyasa hakan zai fi. Ayi mana bayanin abin da ya sa idan kudu ta karbi kujerar shugaban kasa, Arewa da sauran bangarorin Najeriya za su amfana.”
"Najeriya kasa ce da ake siyasa, mutane suna yin zabe. ‘Yan Najeriya a ko ina su ke, za su kada kuri’a. Sai jam’iyyun siyasa sun yi aiki da gaske.”

A baya an ji cewa Kungiyar Arewa ta maida wa Gwamnonin Kudu raddi na cewa mulki zai koma Kudu.

Hakeem Baba-Ahmed ya ja kunnen Gwamnoni cewa ba za su sallama masu mulki a bagas ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel