Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

  • Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya tsame kan sa daga binciken da jami'an tsaro suka shiga gidan Mary Odili suka yi
  • Malami ya ce ba shi da masaniya balle hannu a ciki kuma ma'aikatarsa za ta binciko dalilin wannan samamen da aka kai gidan alkalin
  • A cewar mai magana da yawunsa, ofishin mai girma ministan shari'a ba zai karya doka irin ta yin kutse gidan ta babu takarda ba

FCT, Abuja - Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya ce ba hannun shi balle ofishinsa a dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi a gidan mai shari'a Mary Odili ta kotun koli kuma matar tsohon gwamnan jihar Ribas.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu jami'an tsaro wadanda har yanzu ba a gano ko su waye ba sun shiga gidan alkalin wacce mijin ta ke jerin wanda hukumar yaki da rashawa ke sanye da ido a kan a cikin kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami
Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai kuma, mai magana da yawun hukumar yaki da rashawan, Wilson Uwajaren ya nisanta hukumar da hannu a cikin lamarin, Daily Trust ta wallafa.

Yayin tsokaci kan rahoto da ke alakanta su da samamen, AGF ta bakin mataimakinsa na yada labarai, Dr Umar Jibrilu Gwandu ya ce "Malami ba zai zubar da kansa ba wajen irin wannan lamarin wanda babu wata takardar kotu da ta bayar da damar zuwa bincikar gidanta."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rahotanni kafafen yada labarai sun nuna cewa wannan al'amarin ba zai taba fitowa daga ofishin mai girma antoni janar na tarayya ba da kuma ministan shari'a."

Malami ya kara da cewa ma'aikatarsa za ta bincika tare da gano yadda aka kai samamen da kuma dalilin hakan.

Shugaban EFCC ya magantu kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili

Kara karanta wannan

ICPC: Yadda muka kwato gidaje 301 daga jami'an gwamnati 2 a Abuja

A wani labari na daban, Shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi tsokaci kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidan mai shari'a Mary Odili.

Jami'an tsaro sun shiga gidan alkalin kotun kolin da ke Maitama a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Akwai rahotanni da ke yawo na cewa hukumar EFCC na da hannu kan samamen amma daga bisani hukumar ta tsame kanta daga ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel