Shekaru na 70, amma ba'a taba mumunar gwamnati irin ta Shugaba Buhari ba, Atiku

Shekaru na 70, amma ba'a taba mumunar gwamnati irin ta Shugaba Buhari ba, Atiku

  • Taron gangamin jam'iyyar PDP na cigaba da gudana yanzu haka a dandalin taron Eagle Square dake birnin tarayya
  • Atiku Abubakar ya gabatar da jawabinsa yayinda al'ummar jihar Adamawa suka kada kuri'unsu
  • Atiku yace gaskiya tun da ya zo duniyar nan bai taba ganin mutane sun shiga mugun hali irin wannan ba

Abuja - Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari da APC.

Atiku yace tun da aka haifesa bai taba ganin lokaci da al'umma suka fi kuka saboda tsananin wahala irin yanzu ba, rahoton PT.

Dan siyasan ya bayyana hakan ne jawabin da ya gabatar a taron gangamin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP dake gudana a dandalin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Atiku yace:

"Ba'a taba shiga mumunar hali irin wannan ba a kasar nan. shekaruna 70, kuma ban taba ganin lokaci sa ake shan bakar wahala, rashin tsaro da rashin hadin kai a Najeriya irin wannan ba."
"Muna da daman gyara kasar nan da hada kan kasar nan. PDP ba ma'asumiyar jam'iyya bace, dukkanmu ba ma'asumai bane."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shekaru na 70
Shekaru na 70, amma ba'a taba mumunar gwamnati irin ta Shugaba Buhari ba, Atiku Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

APC cike take da rashawa

Atiku yace jam'iyyar APC ta nunawa yan Najeriya karara cewa cike take da rashawa kuma ba zata itta mulkan kasar nan ba.

"APC ta nuna cewa ba zata iya ba kuma mai rashawa ce. Wajibi ne mu samar da kasar da zata daina nuna kabilanci kuma ta mayar da hankali kan iyawa."

Gwamnatin APC jahila ce

Hakazalika shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan tarayya, Enyinnanya Abaribe, a jawabinsa yace:

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

"Mutane sun kosa wannan kashe-kashe da sace-sacen kudin baitul mali da APC ke yi. Jahilar gwamnati da ta gaza komai yayinda yan bindiga suka mamaye titunanmu."

Akwai bukatar PDP ta dawo mulki

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umari Fintiri, a jawabin da yayi a taron ya bayyana cewa abubuwa basu taba muni a Najeriya ba kamar yadda sukayi a gwamnatin APC.

Yace lallai akwai bukatar jam'iyyar PDP ta koma kan ragamar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel