Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar PDP ta gudunar da taron gangamita, an zabi shugabannin PDP daban-daban a kujerun shugabancin jam'iyya
  • Sabon zababben shugaban jam'iyyar ya bayyana wani sako ga ilahirin shugabannin jam'iyya mai mulki ta APC, ya ce su shirya mika wa PDP mulki
  • Ya bayyana cewa, PDP ta shirya don ceto Najeriya, kuma kasar za ta ci gaba kamar yadda jam'iyyar ta PDP ta tsara

Abuja - Sabon zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya aike da sako ga jam'iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “zamu karbe kasar nan.”

Da yake magana da sanyin safiyar Lahadi bayan zaben sa a taron gangamin jam’iyyar na kasa a Abuja, Ayu ya bayyana shirin jam'iyyar na karbe mulkin kasar a zaben 2023, This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC
Sabon shugaban jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Nan da makonni biyu za ku ga karfin da zai dawo PDP a kowace jiha. Wasu tsirarun mutane sun yanke shawarar raba Najeriya. Za mu hada kan kasar don ci gaban kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun yi a baya, za mu sake yi. Daya jam'iyyar ba za ta taba gudanar d taron gangami ba... kalubale ne. Wannan sanarwar ficewa ce ga dayan bangaren. Zamu karbi kasar. Za mu gina kasa.”

A halin da ake ciki, an samu sakamako na kujeru uku da aka fafata a taron gangamin na jam'iyyar PDP na kasa na 2021.

Bayan zaben da aka yi na neman kujerar mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (kudu), tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya samu kuri’u 705. Ambasada Taofeek Arapaja ne ya lashe zaben da kuri'u 2004.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

A fafatawar da aka yi na shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Suleiman Mohammed Kadede ya yi nasara da kuri’u 3072 inda Usman Elkudan ya samu kuri’u 200. Ambasada Umar Damagom ya samu kuri'u 2234 yayin da Hajiya Ina Ciroma ta samu kuri'u 365.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito adadin jami'an PDP 21 da suka dare manyan kujerun shugabancin jam'iyyar ta PDP.

An zabi wadanda za su fafata a sauran ofisoshi 18 da suka hada da Sakataren jam’iyyar na kasa Sanata Samuel Anyanwu.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ne ya gabatar da kudirin a dage zaman yayin da yake gabatar da wata tawaga domin ceto Najeriya. An kawo karshen taron da karfe 4:30 na safe.

Daga taron gangamin PDP, karshen APC a mulkin Najeriya ya zo, inji wani sanata

A baya kuwa, Shugaban kwamitin karramawa na taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ifeanyi Okowa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, ya ce tsare-tsare da sakamakon atisayen zai tabbatar da cewa jam’iyyar a shirye take ta ceto Najeriya daga kalubalen da ke addabarta.

Kara karanta wannan

Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin

Okowa, wanda shine gwamnan jihar Delta ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron kwamitin da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja.

Ya ce jam’iyyar PDP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa taron zai karfafa hadin kai da dimokradiyya ba a jam’iyyar kadai ba har ma a kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel