Daga karshe: Sabon mamban PDP ya bayyana ra'ayin Atiku kan tsayawa takara a 2023

Daga karshe: Sabon mamban PDP ya bayyana ra'ayin Atiku kan tsayawa takara a 2023

  • Yanzu dai alamu sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku zai sake tsayawa takarar tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a 2023
  • Wani sabon mamban PDP, Dele Momodu, ya ce Atiku kasar ya shaida masa cewa za su hadu a filin wasa, inda ya ce ya ji shahararren dan jaridan na sha’awar tsayawa takara a 2023.
  • Momodu wanda ya koma PDP ya gana da Atiku a taron gangamin jam’iyyar na kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja

Shahararren dan jarida kuma dan siyasa, Dele Momodu, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya kalubalance shi game da zaben shugaban kasa na 2023.

Momodu wanda ya bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasar a taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa a dandalin Eagle Square a ranar Asabar, 30 ga watan Oktoba.

Read also

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Atiku ne ya kalubalance ni na tsaya takarar shugaban kasa, Dele Momodu
Dan jarida kuma dan siyasa, Dele Momodu | Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Momodu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram inda ya bayyana abin da suka tattauna shi da Atiku. Rubutun nasa ya ce:

"Na ji dadi a lokacin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Wazirin Adamawa ALHAJI ATIKU ABUBAKAR ya kalubalance ni da tsayawa takara: "Dele, na ji kana son tsayawa takarar shugaban kasa, za mu hadu a filin wasa... Ka kuma rubuta cewa na tsufa da yawa...
"Na amsa da cewa: "Ranka shi dade, ba zan iya yanke shawara ta bai-daya ba game da takara ba yallabai. Har ila yau, ban ce ka tsufa ba, na ce shekaru ne sanadi kuma akwai matasa da yawa da suka cancanta a Najeriya kuma yaronka da ya amsa batuna ne ya yi aiki mara kyau."
"Alhaji yace bai sa yaron ya rubuta martani ba... Naji dadi sosai da Waziri ya fadi ra'ayinsa cikin walwala..."

Read also

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci

A baya kadan, jaridar The Nation ta rahoto cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai gyara tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba a Abuja yayin gabatar da lacca na cika shekaru 70 da gabatar da littafin Shugaban Kamfanin DAAR Communications Plc, Cif Raymond Dokpesi.

Ya kara da cewa kasar na kuma bukatar jagora wanda zai hada kai, sake fasali da tabbatar da tsaron 'yan kasar.

Source: Legit.ng

Online view pixel