Yanzu-Yanzu: Dele Momodu ya koma jam'iyyar PDP, ya roki yan Najeriya su yafe masa kan taimakawa shugaba Buhari

Yanzu-Yanzu: Dele Momodu ya koma jam'iyyar PDP, ya roki yan Najeriya su yafe masa kan taimakawa shugaba Buhari

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NCP, Dele Momodu, ya shiga babbar jam'iyyar hamayya PDP
  • Sanannen ɗan jaridan ya kuma roki yan Najeriya su yafe masa kuskuren da ya yi na bada gudummuwa har Buhari ya ɗare mulkin Najeriya
  • A cewarsa gwamnatin APC ta baiwa kowa kunya, ta ɓata duk wasu ayyukan alherin da PDP ta gina a lokacin mulkinta

Abuja - Shahararren ɗan jaridan nan, Bashorun Dele Momodu, ya koma babbar jam'iyyar Hamayya PDP, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Momodu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, yayin da yake neman yafiya ga yan Najeriya bisa rawar ta ya taka wajen kawo gwamnatin Shugaba Buhari.

Yace ya ɗauki matakin shiga PDP ne domin bada tashi gudummuwar a haɗa karfi da karfe wajen ceto Najeriya daga rugujewa.

Read also

Tsohon minista tare da daruruwan mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP

Dele Momodu
Yanzu-Yanzu: Dele Momodu ya koma jam'iyyar PDP, ya roki yan Najeriya su yafe masa kan taimakawa shugaba Buhari Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Ina rokon yan Najeriya su yafe mun

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar NCP, ya koka kan halin da Najeriya take ciki yanzun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels tv ra rahoto shi yace:

"Abun takaici da dana sani shine wasu manyan nasarorin da PDP ta yi a mulkinta, yanzun gwamnatin APC ta lalata komai ta ɓata su."
"Ina neman afuwa kan rawar da na taka wajen tabbatar da nasarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015."

Meyasa ya shiga jam'iyyar PDP?

Momodu ya kuma yaba wa mambobin jam'iyyar PDP bisa jajircewarsu da kuma kokarin su duk da irin ƙalubalen da ake fama da shi a kowane mataki.

"Na shigo PDP ne domin kara tallafawa shugabanni da mambobin jam'iyya su ninka kokarin da suke wajen dawo da martabar Najeriya a nahiyar Africa.
"Na yanke shawarar dakatar da wasu abubuwa da suka shafe ni, domin haɗa hannu da masu kishin Najeriya, mu ceto ƙasar daga inda ta dosa."

Read also

Dan Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

"Na yi imanin cewa shigowa siyasa tsundum ne kaɗai zai sa in samu nasarar cimma muradina na ganin Najeriya ta yi kyau."

A wani labarin kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya sake caccakar gwamna Ganduje kan yawan ciyo bashi mara amfani

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yace lokacin da yake gwamna na tsawon shekara 8 bai taba karbo bashin ko naira ɗaya ba.

A cewarsa sai dai ya tarad da bashi ya yi wa jiha katutu lokacin da ya dawo zango na biyu, kuma gwamnatinsa ta biya bashin.

Source: Legit.ng

Online view pixel