Taron gangamin PDP: Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus

Taron gangamin PDP: Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus

  • Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus, ya ce ba ai yarda ba
  • Wannan ya biyo bayan kayen da ya sha gaban kotun daukaka kara a ranar Juma'ar da ta gabata a Fatakwal
  • Dukkan alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani sun yi ittifakin bai da gaskiya

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus, ya lashi takobin garzayawa kotun koli saboda rashin amincewarsa da hukuncin kotun daukaka kara.

A cewarsa, ba zai yarda wasu su ci mutuncin kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba.

Ya ce ba don kansa ya shigar da jam'iyyar kotu ba, kawai ya yi hakan ne domin tabbatar da cewa an bi dokokin demokradiyya.

Secondus ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Mr. Ike Abonyi, rahoton TheNation.

Yace:

"Na umurci lauyoyin na su karanta hukuncin sosai da niyyar daukaka kara da gaggawa saboda ba zan yarda a ci mutuncin kundin tsarin mulkin jam'iyya ba."
"A matsayina na wanda da shi aka gina wannan jam'iyya kuma na rike kujeru daban-daban, na san komai game da yadda jam'iyyar take."

Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus
Taron gangamin PDP: Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus
Asali: Depositphotos

Kotun daukaka kara ta watsawa Secondus kasa a ido

Uche Secondus, dakataccen shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na ƙasa bai yi nasara ba a yunkurinsa na hana yin gangamin taron jam'iyyar na ƙasa, TVC News ta ruwaito.

Secondus ya garzaya kotun daukaka kara ne inda ya ke ƙalubalantar dakatar da shi da aka yi a matsayin shugaban Jam'iyyar na kasa.

Ya kuma shigar da wata bukatar a gaban kotu yana neman a hana ta yin gangamin taron ta Na kasa da ta shirya yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Dukkan alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani sun amince da hukuncin ba tare da jayayya ba.

Gabriel Kolawole wanda ya karanto hukuncin ya ce Secondus bai shigar da kararsa a kan lokaci ba kuma hakan saba dokokin kotu ne.

Kotun daukaka karar ta dora masa laifi na kin shigar da kara a lokacin da aka dakatar da shi a mazabarsa da karamar hukumar har sai yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel