Tsohon minista tare da daruruwan mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP

Tsohon minista tare da daruruwan mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP

  • Tsohon ministan sufuri a tarayyan Najeriya, Ibrahim Bio, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki, ya koma babbar mai adawa PDP
  • Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, ya sauya shekan ne tare da ɗaruruwan magoya bayansa ranar Alhamis
  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara ta bayyana farin cikinta bisa wannan mataki da Bio ya ɗauka, tare da fatan hakan ya haifar da ɗa mai ido

Kwara - Tsohon ministan sufuri a Najeriya, Ibrahim Isa Bio, ya fice daga jam'iyyar APC, ya koma jam'iyyar PDP ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kwara ya sauya shekar ne zuwa PDP tare da ɗaruruwan magoya bayansa a gundumar Gure/Gwasoro, ƙaramar hukumar Baruten, jihar Kwara.

Jam'iyyar PDP
Tsohon minista tare da daruruwan mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP Hoto: bbc.com
Source: UGC

A wata sanarwa da ya fitar a Ilorin, kakakin jam'iyyar PDP reshen Kwara, Tunde Ashaolu, ya yiwa Bio barka da zuwa PDP, tare da yaba masa bisa ɗaukar matakin da ya dace.

Read also

Dan Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Yadda jam'iyyar PDP ta tarbe shi

A sanarwan, Ashaolu yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matakin ya yi dai-dai da muradin al'ummar jihar Kwara, waɗan da ke shirin canza gwamnatin gwamna Abdulrahman Abdulrazaq."
"Muna masu farin cikin yin maraba ga tsohon minista Ibrahim Isa Bio zuwa jam'iyyar PDP."
"Mun yaba da ɗaukar matakinsa na ficewa daga rusasshiyar jam'iyyar APC da bata iya komai ba, ya dawo PDP dake ƙara ƙarfi a kan ƙarfi kowace rana."

Abinda sauya shekarsa zai kara wa PDP

Kakakin PDP ya kara da bayyana fatansa cewa sauya shekar Bio zai ƙara wa jam'iyya karsashi, kasancewarsa shugaban da ake ganin girmansa kuma kwararren ɗan siyasa.

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan APC tare da dubbannin magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Benuwai.

Read also

Rikicin cikin gida: Jam'iyyar Hamayya PDP ta dakatar da manyan jiga-jiganta 10

Sanata Abba Moro, yace jam'iyyar PDP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya daga halin da APC ta jefa ta idan ta samu dama a 2023.

Sanatan, wanda ya yi jawabi wajen bikin tarbar masu sauya sheƙan, yace Najeriya ta rasa komai ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Source: Legit.ng

Online view pixel