Ina gwamna ban taba karbo bashin ko kwandala daya ba, Kwankwaso ga Ganduje

Ina gwamna ban taba karbo bashin ko kwandala daya ba, Kwankwaso ga Ganduje

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnan Kano, Dakta Ganduje, kan maida Kano mai fama da bashi
  • Tsohon gwamnan Kano yace lokacin da yake matsayin gwamna. na tsawon shekara 8 bai taba karbo bashi ba
  • A cewarsa sai dai ya tarad da bashi ya yi wa jiha katutu lokacin da ya dawo zango na biyu, kuma gwamnatinsa ta biya bashin

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yace lokacin da yake gwamna na tsawon shekara 8 bai taba karbo bashin ko naira ɗaya ba.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya faɗi haka ne yayin fira da kafar watsa labarai na Arise TV ranar Jumu'a da safe.

Ya kuma zargi Gwamnan Kano na yanzu, Dakta Abdullahi Ganduje, da jefa jihar cikin ƙaƙani kayin bashi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

Sanata Kwankwaso
Ina gwamna ban taba karbo bashin ko kwandala daya ba, Kwankwaso ga Ganduje Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Menene amfanin ciyo bashi?

Kwankwaso, wanda shine shugaban tafiyar Kwankwasiyya, yace mafi yawan ayyukan da gwamnan ke yi da kuɗaɗen bashin sam ba su zama dole ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoto The Cable, Yace:

"A tafiyar kwankwasiyya ba mu yarda da karɓo bashi ba, sai dai idan abinda za'ayi ya zama wajibi. Kuma ina mai alfaharin cewa lokacin ina gwamna daga 1999 zuwa 2003 ban taba cin bashin ko naira ɗaya ba."
"Maimakon haka ma mun biya bashin da wasu suka ciyo mana ne. Haka nan lokacin da na sake komawa kan mulki a 2011, mun samu bashi da yawa da aka karɓo kafin zuwan mu."
"Aƙalla an karbo bashin dala miliyan $200m daga bankin duniya kan wasu abubuwa kamar zazzabin Malaria, na baiwa kwamishina umarnin ya sasanta da bankin, kuma mun warware shi baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Naɗa ɗan shekara 66 shugaban kwamitin soshiyal midiya ya janyo cece-kuce

A wani labarin kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Rabiu Kwankwaso, yace Ganduje ya bashi kunya kan ayyukan da yake a matsayin gwamna

Ya ce duk da cewa ba shi da wata matsala tsakaninsa da Ganduje amma bai gamsu da irin ayyukan da ya yi ba.

Kwankwaso ya yi wannan furucin ne a lokacin da wasu masu nazarin siyasa ke ganin akwai yiwuwar ya shirya da Gandujen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel