Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma PDP

Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma PDP

  • Ilahirin mabiya tsohon gwamnan Oyo sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP bayan wata doguwar tattauanawa da shugabansu
  • A jihar Oyo ne aka yi tattaunawar da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP hudu suka halarta tare da shugaban jam'iyyar ZLP
  • Tun a baya wasu jiga-jigan PDP sun hango yiyuwar komawar gwamnan jam'iyyarsu, inda suka bayyana balo-balo a kafafen yada labarai

Oyo - Jiga-jigan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a jihar Ondo sun yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.

An cimma matsayarsu ta komawa jam'iyyar PDP ne a wani taro da aka yi a garin Ondo da shugaban jam'iyyar ZLP na kasa Dr. Olusegun Mimiko.

Wannan dai shi ne karo na uku da Mimiko zai sauya sheka zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Sheikh Abduljabbar ya sake rikici da Lauyoyinsa a Kotu, Yace basu da cikakken ilimin kare shi

Ganawar gwamnonin PDP da mambobin ZLP
Bayan ganawar gwamnonin | Hoto: Alade Sam Olusegun
Asali: Facebook

Sauran shugabannin ZLP da suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin gwamnan Ondo Agboola Ajayi; Hon Gboye Adegbenro da tsohuwar kakakin majalisar Ondo Jumoke Akindele.

Hakazalika da shugaban ZLP na Ondo, Hon Joseph Akinlaja; Tsohon dan takarar gwamna Banji Okunomo da kuma tsoffin manyan hadiman Mimiko.

Tsohon Gwamnan wanda ya yi wata ganawar sirri da gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Seyi Makinde, ya ce an gayyaci jam’iyyar ZLP ne domin su shiga jam’iyyar PDP da nufin ceto kasar nan daga kangin rashin tsaro.

Ya bayyana cewa taron an yi shi ne domin cudanya da ‘ya’yan jam’iyyar a sakamakon jerin mu’amalar da suka yi da shugabannin PDP bisa gayyatar da aka yi masu.

Tsohon Gwamnan na Ondo ya ce shugabannin jam’iyyar PDP sun nuna kwarin gwiwa wajen hada kan duk wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar ta ZLP tare da ba su cikakken ‘yancin zama ‘yan PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP hudu sun dira jihar Ondo da nufin zawarcin tsohon gwamna jihar

Bayan tattaunawar ne, Hon Akinlaja ya bukaci a gabatar da kudirin neman ‘yan jam’iyyar ZLP na jihar Ondo su koma jam’iyyar PDP, wanda tuni aka amince gaba daya.

Yadda gwamnonin suka dira jihar Oyo zawarcin 'yan ZLP

Gwamnonin jam'iyyar PDP hudu sun isa jihar Ondo domin ganin tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko ya dawo jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Dimbin ‘ya’yan jam’iyyar ZLP sun hallara a gidan Mimiko da ke garin Ondo domin tarbar tawagar jam’iyyar PDP karkashin jagorancin gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Sauran Gwamnonin da ke cikin tawagar akwai Nyesom Wike na jihar Ribas; Okezie Ikpeazu na jihar Abia and Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

A wani labarin, Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Wata kungiyar mata ‘yan siyasa ta Women in Politics Forum (WIPF), a jiya Laraba ta yi barazanar kai karar jam’iyyar PDP, kan wani shiri na mayar da mata bare a taron gangaminta na kasa da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby"

Kungiyar ta yi zargin cewa jam’iyyar na kokarin kefe mata a yayin taron gangamin da aka shirya gudanarwa a tsakanin ranakun 30 zuwa 31 ga watan Oktoba, 2021 ta hanyar samar da wani tsari na bai daya da ya karkata wajen ganin maza su raba mukaman jam’iyyar.

Wannan, a cewarsu, ya saba kaso 35 na tabbatar da matakin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel