Masu Zanga-Zangar Sun Yiwa Sakatariyar Jam’iyyar APC Kawanya, Suna Neman a Tsige Shugaban Jam’iyyar Na FCT

Masu Zanga-Zangar Sun Yiwa Sakatariyar Jam’iyyar APC Kawanya, Suna Neman a Tsige Shugaban Jam’iyyar Na FCT

  • Dandazon matasa; maza da mata ne suka mamaye sakateriyar APC a yau Talata 18 ga watan Oktoba domin mika kokensu ga shugaban jam'iyya
  • Matasa sun nemi Sanata Abdullahi Adamu ya yi musu bayani tare da tsige shugaban APC na babban birnin tarayya
  • Jam'iyyar APC na ci gaba da gangami a kasar nan domin tallata 'yan takara, jiga-jiganta na ci gaba da kushe sauran 'yan takara

FCT, Abuja - Daruruwan masu zanga-zanga ne suka mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a ranar Talata, inda suke neman a tsige shugaban jam'iyyar na babban birnin tarayya, Abdulmalik Usman, rahoton Vanguard.

Masu zanga-zangar da suka hada da matasa; maza da mata, sun bayyana cewa, dole a amince da zaben da aka yi na shugabancin jam'iyyar na 2021, kuma dole a tsige Usman daga mukaminsa saboda kin karbar sabbin shugabanni a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Mun daina aikata zunubi saboda Atiku ya lashe zaben 2023

Matasan APC sun yi zanga-zanga, suna neman a tsige shugaban APC na FCT
Masu Zanga-Zangar Sun Yiwa Sakatariyar Jam’iyyar APC Kawanya, Suna Neman a Tsige Shugaban Jam’iyyar Na FCT | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Dandazon matasan sun mamaye sakateriyar APC ne da sanyin safiyar yau Talata 18 ga watan Oktoba, inda suka dagula lamurran yau da kullum tare da neman jin ta bakin shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu kan batun tsige Usman.

Koken da matasan suke gabatarwa

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, an ga matasan dauke da allunan zanga-zanga dake nuna adawa da shugabancin Usman, tare da yin kiraye-kiraye da kakkausar murya wajen tsige shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsu, tsige shugaban na APC a FCT ne kadai zai warkar da gyambon dake kara ruba a jikinsu, inda suka ce dole a yi musu adalci.

A bangare guda, matasan da suka dura sakateriyar jim kadan bayan isan Sanata Abdullahi Adamu ofis, sun zarge shi da karbar cin hanci daga wasu 'yan siyasar PDP a FCT don tabbatar da jam'iyyar ta adawa ta lashe zaben 2023 a birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya bayyana cewa:

"Muna son ganin Adamu. Dole ya dakatar da cin amanar ta hanyar tabbatar da ba a rantsar da Abdulmalik a wa'adi na uku ba. Idan kuwa ya gaza yi mana bayani, kenan hakan na nufin ya karbi cin hanci daga PDP don ganin APC ta rasa zaben 2023 a FCT."

Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana a wani faifan bidiyon da TVC ta yada, inda yake bayyana kadan daga abu mara dadi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya yi masa.

Ya tuna cewa, a shekarar 2013, ya kai ziyarar duba zabe a jihar Anambra, a nan ne dai Obi ya tsare shi tare da kokarin tozarta shi saboda a lokacin baya rike da mukamin gwamna.

A cewarsa, yanzu kuma shine gwamna a jihar Kaduna, gashi kuma Peter Obi, wanda a yanzu dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour zai shigo jiharsa, amma ba zai masa komai ba saboda shi wayayye ne kuma mai sanin ya kamata, cikakken dan Arewa.

Kara karanta wannan

Tashin hakali: 'Yan kwangilar maganin yaki da Korona sun tsoho ma'aikata a Abuja, suna zanga-zanga

Asali: Legit.ng

Online view pixel