2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna

2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna

  • Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom yana da yakinin cewa jam'iyyar PDP za ta dawo mulki a Najeriya a shekarar 2023
  • Gwamna Emmanuel ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun koyi darasi bayan zaben jam’iyyar APC a zaben 2015 da 2019.
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron da jam’iyyar PDP ta shirya domin fara rijistar ‘ya’yanta ta yanar gizo

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel ya ce akwai fatan alheri ga ‘yan Najeriya idan aka yi la’akari da gagarumin nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a matsayin jam’iyya a kasar.

Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a Uyo, yayin da yake kaddamar da rajistar ranar gizo na mambobin jam’iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP

Ya yi nuni da cewa irin kukan da ‘yan Nijeriya ke yi a halin yanzu saboda rashin shugabanci nagari, za a iya magance shi ta hanyar shugabanni masu kishin jama’a da jam’iyya irin ta PDP ke da su.

2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, gwamna Udom
Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar PDP | Hoto: Akwa Ibom PDP
Asali: Facebook

A cewar Gwamna Emmanuel, wahalhalun da ake fama da su a Najeriya a halin yanzu, nuni ne na rashin shugabanci na gari na gwamnatin da wasu ‘yan Najeriya suka dora, wanda ya ce ya tabbatar da ingancin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa PDP za ta samar da kyakkyawan sakamako na shugabanci idan da har yanzu tana rike da madafun iko a matsayinta na jam’iyya.

A kalamansa:

“Idan ba mu bar Najeriya ta gwada wata jam’iyya ba, da a yau hayaniyar ta yi yawa. Wasu ‘yan Najeriya sun so “canji” yau, sun ga inda canjin da ya kawo mu.

Kara karanta wannan

Wike ya yi kaca-kaca da mulkin Buhari, yace abubuwa ba su taba tabarbarewa haka ba

"Amma ina fatan Najeriya za ta yi kyau fiye da yadda ake tsammani idan jama'a za su sake ba PDP dama."

Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai gyara tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba a Abuja yayin gabatar da lacca na cika shekaru 70 da gabatar da littafin Shugaban Kamfanin DAAR Communications Plc, Cif Raymond Dokpesi.

Ya kara da cewa kasar na kuma bukatar jagora wanda zai hada kai, sake fasali da tabbatar da tsaron 'yan kasar.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya ce shi ne mutumin da ya dace da zai ba kasar abin da take bukata.

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa

A bangare guda, Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel