Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP

Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce nan ba da dadewa ba manyan ‘yan jam’iyyar APC za su sauya sheka
  • Saraki ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin din Arise su ka yi da shi a ranar Talata
  • Tsohon gwamnan jihar Kwara ya ce dama PDP ba ta yi mamakin yadda wasu gwamnonin PDP su ka dinga komawa APC ba

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Bisa ruwayar The Cable, Saraki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Arise TV ta yi da shi ranar Talata.

Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP
Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP, Inji Saraki
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya bayyana cewa dama PDP ba ta girgiza ba da sauya shekar da wasu gwamnonin PDP su ka yi zuwa APC, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani dan majalisa ya koma jam'iyyar PDP ana saura kwana 11 zabe a Anambra

Gwamnoni kamar Ben Ayade na Cross River, Dave Umahi na jihar Ebonyi da Bello Matawalle na jihar Zamfara sun koma jam’iyya mai mulki.

A cewar sa ‘yan Najeriya sun fara ganin yadda ake sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki, kuma kwanan nan shugabannin jam’iyya mai mulki za su fara sauya sheka a kurarren lokaci.

Tsohon shugaban majalisar dattawar ya ce:

“Kada ku yi tunanin mu (PDP) mu na jin haushi. Idan ba ku manta ba, na dade da cewa wasu gwamnoni za su sauya sheka kuma sun sauya. Kuma ba mu yi mamaki ba."

Akwai manyan mutane a APC da za su koma PDP

Akwai manyan mutane da za su shigo jam’iyyar mu. A wannan makon akwai tsohon gwamnan da zai shiga jam’iyyar. Akwai wadanda su ka koma dama.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigai da mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar

“Mun san cewa shugabanni ba sa sauya sheka sai a kurarren lokaci. Ba sa komawa da wuri. Kada ‘yan Najeriya su yi mamaki idan su ka ga wasu shugabanni a jam’iyya mai mulki sun sauya sheka,” - a cewar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel