Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

  • Rikicin PDP na kara kamari yayin da jam'iyyar ta hana wasu mambobinta tsayawa takara
  • An dakatar da su ne daga takarar gabanin babban taron gangamin da ke tafe a nan gaba kadan
  • An ce, mambobin sun kai jam'iyya kaea a gaban kotu domin a dakatar da babban taron gangaminta

Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP ya hana 'yan takara uku tsayawa takarar mukamai a kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Wadanda ba su cancanta ba da mukaman inji PDP sun hada da: Farfesa Wale Oladipo (Osun) wanda ya nuna sha’awarsa ga mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu.

Da Duminsa: PDP ta hana wasu fitattun 'yan takara tsayawa takarar shugabancin PDP
Jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika da Okey Muo-Aroh (Anambra) wanda ya nuna sha’awar matsayin Sakataren Kasa Dakta Olafeso Eddy (Ondo) Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

Shugaban Kwamitin shirya taron gangami, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da tambari na taron gangamin kasa na 2021 da kayayyakin talla, a Sakatariyar PDP ta Kasa, Abuja a ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce 'yan takarar ba su cancanci shugabancin jam'iyyar ba saboda shigar da jam'iyyar kotu don dakatar da taron gangami.

A cewar Gwamnan, wadanda ba su cancantan ba sun kasa murkushe tsarin warware rikice-rikicen cikin gida kamar yadda tsarin mulkin PDP ya tanadar

Ya sanar da cewa an tsayar da wasu 'yan takara 27 don takara a taron gangamin yayin da daya ya janye daga takarar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rikici a APC yayin da aka rantsar da 'yan wani tsagi bayan taron gangami a Ribas

A bangare jam'iyyar APC mai mulki kuwa, rikicin da ya barke a cikin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ya dauki wani sabon salo na daban.

Kara karanta wannan

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

Jaridar The Punch ta rahoto cewa bangaren da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe a ranar Talata 18 ga watan Oktoba, ya kaddamar da babban jami’in gudanarwar sa.

A cewar rahoton, an yi bikin ne a Freedom House, sakatariyar yakin neman zaben da Sanata Abe ya kafa a GRA ta Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel