Yanzu-yanzu: Uche Secondus garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa

Yanzu-yanzu: Uche Secondus garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa

  • Uche Secondus, dakataccen shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya garzaya kotu yana neman a hana jam'iyyar yin taron gangami
  • Secondus ta bakin lauyansa ya bukaci a hana yin taron gangamin har sai bayan an yanke hukuncin karshe kan daukaka karar da ya shigar
  • Kotu ta raba da Secondus ta kujerarsa ne bayan da wasu suka yi kararsa a kotu amma shima ya daukaka kara yana kuma jiran hukunci

Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na kasa, Uche Secondus ya bukaci jam'iyyar ta dakatar da shirye-shiryen da ta ke yi don gudanar da gangaminta na kasa, rahoton Daily Trust.

Tuni dai, jam'iyyar ta fara shirye-shiryen gudanar da taron da za a yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoban 2021.

Yanzu-yanzu: Secondus garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa
Yanzu-yanzu: Secondus garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

Amma cikin wasika da ya aike wa jam'iyyar ta hannun lauyansa, Tayo Oyetibo, SAN, Secondus ya bukaci kotu ta hana jam'iyyar yin taron har sai an yanke hukuncin karshe kan daukaka kara da ya yi.

Wani sashi na wasikar ya ce:

"A ranar 23 ga watan Agustan 2021, wani Mr Ibeawuchi E. Alex da wasu su hudu sun shigar da kara mai lamba PHC/2183/CS/2021 a kotun jihar Rivers kan Prince Uche Secondus da PDP.
"A ranar 10 ga watan Satumban 2021, babban kotun ta yanke hukunci game da karar inda ta dakatar da Prince Uche Secondus a matsayinsa na Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa."
"An shigar da kara a kotun daukaka kara da ke Port Harcourt. Kazalika, an rubuta wa kotu takarda inda Prince Uche Secondus ke neman kotu ta hana PDP, ko jami'anta, 'ya'yanta ko wakilanta yin taron gangamin da ake niyyar yi a ranar 30 da 31 ga watan Oktoba ko wani ranar, har sai an yanke hukunci kan daukaka kararsa."

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Secondus ya nemi PDP ta mayar da shi kan kujerarsa sai an yanke hukunci

Bugu da kari, Secondus ya kuma nemi jam'iyyar ta barshi ya koma kujerarsa ta shugaban jam'iyyar na kasa kamar yadda ya ke kafin 22 ga watan Agusta, har sai lokacin da aka yanke hukunci kan daukaka karar da ya yi.

A cewar wasikar, tuni dai an raba wa dukkan wadanda aka yi karar a kotu wannan sabuwar bukatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel