Gwamna ya gwangwaje Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100 don ya daina sukar Buhari

Gwamna ya gwangwaje Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100 don ya daina sukar Buhari

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya gwangwaje Father Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100
  • Sai dai, ya yi kira ga fitaccen faston da ya daina caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda kokarin da ya ke yi a kasar nan
  • Ya kai wannan kyautar ne inda ya samu rakiyar gwamnonin kudu maso gabas yayin bikin girbi na shekarar nan

Enugu - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya yi kira ga daraktan Adoration Ministry Enugu, Rabaren Father Ejike Mbaka da ya daina caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi wannan kiran ne yayin bikin girbi na wannan shekarar tare da nuna godiya ga shugaban Adoration Ministry a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba.

Gwamna ya gwangwaje Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100 don ya daina sukar Buhari
Gwamna ya gwangwaje Mbaka da N30m, doya 200 da buhun shinkafa 100 don ya daina sukar Buhari. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Kamar yadda The Punch ta wallafa, Umahi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ya samu rakiyar Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Kara karanta wannan

2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya

Umahi ya bada naira miliyan talatin, doya guda dari biyu da kuma buhunan shinkafa kuma ya sanar da cewa Buhari na aiki wurin gyara tattalin arzikin kasar nan tare da rage fatara a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya shawarci cewa "wadanda aka zaba domin shugabanci a kasar nan ya dace su samar da shugabanci nagari ga talakawan da suka zabe su."

Kamar yadda Umahi, gwamnoni, Ohanaeze Ndigbo da sauran fitattun jama'ar yankin suka ce, su na kokarin ganin an sako shugaban 'yan awaren masu kafa kasar Biafra, Mazi Nnamdi Kanu nan babu dadewa.

Babu shakka Mbaka ya goyi bayan Buhari a yayin gangamin zabensa karo na farko, sai dai daga baya ya fara caccakar shugaban kasan kan halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, LIB ta ruwaito.

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

Kara karanta wannan

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

A wani labari na daban, Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci malaman kudancin kasar nan da su tashi tsaye wurin tattaunawa da masu tada kayar baya tare da assasa rashin tsaro a yankunansu kamar yadda ya ke wa 'yan bindiga.

Fitaccen malamin ya sanar da hakan ne yayin da ya ke fitar da takarda kan martaninsa ga masu bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sake bukatar gwamnatin tarayya da ta bayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda. Tsokacin gwamnan ya janyo cece-kuce daga wurin jama'a daban-daban kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel