Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

  • Ghali Umar Na'Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai ya ce Buhari ya gaza ne saboda ba ya neman shawarar kowa
  • A cewar Na'Abba, arewacin Najeriya ba ta mori komai game da shugabancin Muhammadu Buhari ba a yankin
  • Ya ce hakan ce ke sa 'yan arewa ke fatan mulki ya zauna yankin domin kuwa gani suke asarar shekaru takwas din Buhari za su yi

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'Abba, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza neman shawara kuma hakan yasa ya kasa shawo kan matsalar Najeriya.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a Trust TV, gidan talabijin na Media Trust, mawallafan jaridar Daily Trust.

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara
Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce, a shekaru shida da suka gabata, shugaban kasan ya ware kansa daga abubuwan da ke faruwa, hakan ya kawo kokwanto a cikin zukatan 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

"Ba za ka iya shugabantar kasa ta haka ba, ya dace a ce kana jin ra'ayoyi. Kuma wannan ra'ayoyin ba su da alaka da jama'a, idan kuwa ya taba jama'a da walwalarsu ne toh ina ganin hakan ya dace," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na'Abba ya ce hatta jama'ar arewa ba su gamsu da tsarin shugabancin shugaba Buhari ba wanda ya ce bai taimaki jama'ar yankinsa da komai ba, Daily Trust ta ruwaito.

"A arewacin Najeriya a yau, shawarar da wasu ke bayarwa kan cewa sai an mika shugabancin kasa wani yankin ba ya yi wa wasu dadi saboda a tunaninsu shekarun da Buhari ya yi duk bacin lokaci ne.
"Babu abinda suka karu da shi. Don haka a kan mene jama'a za su dinga batu kan shugabanci ya bar yankin?
“Amma kuma abinda nake kara tambaya shine, me zai sa a sake zaben wani shugaban kasa daga yankin arewa," yace.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Tsohon kakakin majalisar ya ce, ba kamar jam'iyyar PDP ba, shugaban kasa ya kasa neman shawara kan manyan matsalolin kasar nan, hakan yasa ya gaza.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel