2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya

2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya

  • Shahararren mawakin Buhari, Dauda Adamu Kahutu zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya wanda zai wakilci mazabun Bakori da Danja
  • Rarara ya ce zai tsaya takarar wannan kujera idan har ya kammala aikin da ke gabansa, amma ya ce idan hakan bai samu ba toh a nan gaba.
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mawakin na shugaban kasa ya ce zai so a kara wa Shugaba Buhari wa'adin shugabancin kasar

Katsina - Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar dan majalisar tarayya wanda zai wakilci mazabun Bakori da Danja.

A wata hira da yayi da jaridar Leadership Hausa, shahararren mawakin na shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gaskiya ne rade-radin da ke ta yawo kan haka.

Kara karanta wannan

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya
2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya Hoto: thenewsnigeria.com.ng
Asali: UGC

Rarara ya kuma sanar da cewa akwai sabuwar wakar da ya yi bayan talakawa sun biya shi inda suka nemi a bayyana ayyukan shugaban kasar, ya kuma ce a kwanan nan zai ziyarci jihohin kasar domin hasko irin ayyukan da Buhari yayi.

Jaridar ta kuma rahoto cewa Rarara ya ce ya yi niyyar zakulo ayyuka 90 da shugaban kasar yayi amma sai ya gano dubu 900 wanda yake ganin aikin yana da yawa.

Saboda haka ya ce idan har ya samu dama ya kammala wannan aiki nasa toh zai koma kan batun tsayawarsa takara wanda tuni ya ce ya fara yawo a gidajen siyasa.

Ya ce:

“Idan Allah ya nufa na gama wannan aiki da ke gaba na, toh zan tsaya takarar dan majalisar tarayya na mazabun Bakori da kuma danja, idan kuma wannan aiki ya sha gaba na, sai dai kuma a gaba.”

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: An tura mahaifi na gidan yari don ya ƙi yarda in yi makarantar boko

Rarara ya bada shawarar a kyale Buhari ya cigaba da mulki har zuwa shekarar 2027 ko 2028

A gefe guda, mun kawo a baya cewa, Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara, ya yi hira ta musamman da BBC Hausa, inda ya tabo batutuwan siyasa da yadda yake shirya wakoki.

Shahararren mawakin ya bayyana cewa akwai bukatar a bar Muhammadu Buhari ya cigaba da mulki.

Da yake bayanin rayuwarsa, an ji cewa an haifi fitaccen mawakin ne a garin Kahutu, karamar hukumar Danja, a jihar Katsina, ya kuma dade a waka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel