Da dumi: Uwar jam'iyya ta watsawa Shekarau kasa a ido, ta ce zaben Abdulahi Abbas kadai ne zaben da ta sani

Da dumi: Uwar jam'iyya ta watsawa Shekarau kasa a ido, ta ce zaben Abdulahi Abbas kadai ne zaben da ta sani

  • Hedkwatar APC a Abuja tace zabe daya ta sani aka yi a jihar Kano
  • An tura kwamitin mutum biyar na musamman don sulhu tsakanin 'yayan jam'iyyar
  • An samu rabuwar kai tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Kano

Jihar Kano - Mambobin Kwamitin da uwar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta tura jihar Kano sulhunta 'yayan jam'iyya sun dira kum sun fara aikinsu.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa uwar jam'iyyar APC ta tura mutum biyar daga Abuja domin sauraron korafe-korafen 'yayan jam'iyyar bisa zaben shugabannin da akayi makon da ya gabata.

Da dama an yi tunanin cewa wannan zaman sulhu za'a yi ta ne tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da Malam Shekarau.

Amma yayin kaddamar da aiki daga dira Kano, shugaban kwamitin, Tony Macfoy, ya bayyana cewa korafe-korafe kan aben da akayi a dakin taron filin Sani Abacha, wanda Abdullahi Abbas yai nasara kadai zasu saurara.

Kara karanta wannan

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

Da dumi: Uwar jam'iyyar APC ta watsawa Shekarau kasa a ido
Da dumi: Uwar jam'iyya ta watsawa Shekarau kasa a ido, ta ce zaben Abdulahi Abbas kadai ne zaben da ta sani Hoto: Abdullahi Abbas
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, uwar jam'iyya zabe daya ta san an yi a Kano, wanda Gwamna Ganduje ya jagoranta kuma Abdullahi Abbas ya zama shugaba.

Ya yi bayanin cewa kwamitinsu za ta zauna na tsawon kwanaki uku, daga yau Asabar zuwa ranar Litinin daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a Sakatariyar jam'iyya dake Kano.

Rabuwar kai a APCn Kano: Shekarau da mabiyansa kawai so suke a dama dasu, za'ayi sulhu: Cham Faliya

Mamban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Cham Sharon Faliya, ya bayyana cewa abinda ke faruwa a Kano ba bakon abu bane a siyasar Najeriya.

Sharon, wanda yana daya daga cikin mutum 7 da uwar jam'iyyar daga Abuja ta tura gudanar da zaben shugabannin APC a jihar Kano ya bayyana hakan a hirarsa da Legit Hausa.

Kara karanta wannan

Alhassan Doguwa da 'Kwamanda' Sule Garo sun yi musayar yawu a Kano

Ya bayyanawa wakilin Legit cewa tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai ci, Malam Ibrahim Shekarau, la'alla sun hangi wani abu ne wanda ka iya zama cikas garesu nan gaba shi yasa suka tada jijiyoyin wuya.

Mr Sharon Faliya ya cigaba da cewa ba zasu so wannan lamari ya kai ga kotu ba amma ba wai suna tsoron haka bane.

A cewarsa ko kotu aka je, shugabannin APC da aka zaba a zaben da kwamitinsu ta shirya za'a baiwa nasara duk da cewa ba zasu so hakan ya faru ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel