Rabuwar kai a APCn Kano: Shekarau da mabiyansa kawai so suke a dama dasu, za'ayi sulhu: Cham Faliya

Rabuwar kai a APCn Kano: Shekarau da mabiyansa kawai so suke a dama dasu, za'ayi sulhu: Cham Faliya

  • Mamban kwamitin uwar jam'iyyar da ta shirya zaben shugabanni a Kano yace tabbas za'a shawo kan Malam Shekarau da mabiyansa
  • Sharon Cham yace wannan ba bakon abu bane a siyasar jihar Kano
  • Ya kara da cewa nan da yan makonni Mai Mala Buni zai dinke barakar

FCT Abuja - Mamban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Cham Sharon Faliya, ya bayyana cewa abinda ke faruwa a Kano ba bakon abu bane a siyasar Najeriya.

Sharon, wanda yana daya daga cikin mutum 7 da uwar jam'iyyar daga Abuja ta tura gudanar da zaben shugabannin APC a jihar Kano ya bayyana hakan a hirarsa da Legit Hausa.

Ya bayyanawa wakilin Legit cewa tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai ci, Malam Ibrahim Shekarau, la'alla sun hangi wani abu ne wanda ka iya zama cikas garesu nan gaba shi yasa suka tada jijiyoyin wuya.

Read also

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

A cewarsa:

"Abin da nake gani ke faruwa a siyasar Kano, Shi Malam Shekarau da mabiyansu la'alla sun fahimci cewa mai girma gwamna akwai inda ya dosa, kuma inda ya dosa ba dasu ake tafiya ba. Shiyasa suka tashi."

Bamu fatan wannan abu ya kai kotu, za'ayi sulhu

Mr Sharon Faliya ya cigaba da cewa ba zasu so wannan lamari ya kai ga kotu ba amma ba wai suna tsoron haka bane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa ko kotu aka je, shugabannin APC da aka zaba a zaben da kwamitinsu ta shirya za'a baiwa nasara duk da cewa ba zasu so hakan ya faru ba.

Yace:

"A matsayina na dan jam'iyya, ba fata na bane in ga wannan ta zama maganan kotu. Ina da karfin gwiwa cewa shugabanninmu na jam'iyya zasu nemi zama da su a shawo kansu."

Read also

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

"Ni na san su Malam Shekarau sun yi haka ne domin ya zaman musu karfin neman ayi tafiya dasu. Idan tafiya tayi tafiya za'a yi haka."
"Maganan kotu ba fata bane aje kotu koda yake koda an je kotu, akwai hujjoji cewa mu aka rantsar kuma mu muka gudanar da wannan zaben, amma a siyasance ba za'a je kotu ba. Dole ne za'a nemi hadin kansu a san ya za'ayi."

Rabuwar kai a APCn Kano: Shekarau da mabiyansa kawai so suke a dama dasu, za'ayi sulhu: Cham Faliya
Rabuwar kai a APCn Kano: Shekarau da mabiyansa kawai so suke a dama dasu, za'ayi sulhu Hoto: Cham Sharon Faliya
Source: Facebook

Wani mataki shugaban rikon kwarya Mai Mala Buni zai dauka?

Yayinda muka tambayesa kan wani mataki uwar jam'iyya da kanta ke dauka kan ire-iren wadannan rikice-rikice, ya bayyana cewa nan da yan makonni duk za'a shawo kansu.

A cewarsa:

"Sauran rikice-rikicen nan da kake gani a jihohi, matsala ne na 'yayan jam'iyya na cikin gida kamar dai na irin Kano."
" Tun da muna da imani Mai Mala Buni mutum ne mai kokarin kwantar da rikici a siyasa. Tafiyarsa ta sha banban da na mulkin Oshiomole. Oshiomole lokacin bai ki yai ta kunnanwa kowa ashar ba. Amma Mai Mala Buni nan da makonni zai bi wadannan kungiyoyi duk ya kwantar musu da hankali don shi ba mai kace-nace bane."

Source: Legit.ng

Online view pixel