Alhassan Doguwa da 'Kwamanda' Sule Garo sun yi musayar yawu a Kano

Alhassan Doguwa da 'Kwamanda' Sule Garo sun yi musayar yawu a Kano

  • Wani sabon abu na faruwa tsakanin 'yayan gidan siyasan gwamnan jihar Kano
  • Jigogin jam'iyyar APCn biyu a Kano sun yi musayar kalamai a wani taro
  • Wannan abu ya gudana gaban uwargidar gwamnan jihar, Farfesa Hafsat

Kano - Biyu daga cikin manyan jiga-jigan siyasa kuma mabiya gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sun yi musayar yawu gaban uwargidan gwamna, Farfesa Hafsat Ganduje.

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, da kwamishanan kananan hukumomi, Murtala Sule-Garo wanda aka fi sani da Kwamanda sun samu sabani ne a taron raba kayan tallafi a karamar hukumar Tudun Wada.

A cewar rahoton Daily Trust, Sule Garo a jawabinsa ya yiwa Doguwa jawabin 'hannunka mai sanda' inda yace Allah ya sa wannan tallafi da ya baiwa mutane dan Allah aka yi ba dan wata manufa ba.

Kara karanta wannan

Yan IPOB sun kai hari ofishohin yan sanda 164, sun kashe jami'ai 175, duka laifin Nnamdi Kanu ne: FG

Wannan magana ta batawa Doguwa rai kuma kai tsaye ya umurci hadimansa su jibge kudade N70million gaban uwargidar Gwamna.

An gayyaci uwargidar gwamnan taron ne matsayin babbar bakuwa.

Daga karshe, Hajiya Hafsat Ganduje tayi kokarin kwantar da kuran inda ta jinjinawa Ado Doguwa kuma tace lallai nan gaba zai zama Kakakin Majalisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alhassan Doguwa da 'Kwamanda' Sule Garo sun yi musayar yawu a Kano
Alhassan Doguwa da 'Kwamanda' Sule Garo sun yi musayar yawu a Kano Hoto: Facebook/Doguwa
Asali: Facebook

‘Dan Majalisar APC ya rabawa mutane 2000 a mazabarsa kudi da kayan sana'a a Kano

Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya raba kudi da kuma wasu kyauttuka ga mutanen mazabarsa.

Daily Trust tace ‘dan majalisar mai wakiltar yankin Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano ya tallafa wa matasa da mata sama da 2000 a mazabar ta sa.

Alhassan Ado Doguwa ya kashe Naira miliyan 70 a kan mutanen da yake wakilta a majalisar tarayya.

Daga cikin kayan da aka raba wa al’ummar garuruwan Doguwa da Tudun Wada akwai kekunan dinki na wuta 500, da kuma kekunan dinki na kafa 500.

Asali: Legit.ng

Online view pixel