‘Dan Majalisar APC ya rabawa mutane 2000 a mazabarsa kudi da kayan sana'a a Kano

‘Dan Majalisar APC ya rabawa mutane 2000 a mazabarsa kudi da kayan sana'a a Kano

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya gwangwaje mutanensa da kyaututtuka da-dama
  • Honarabul ya raba babura, kekunan dinki da takin zamani a T/Wada da Doguwa
  • ‘Dan Majalisar yace ya yi haka ne domin ya gode wa goyon bayan da yake samu

Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya raba kudi da kuma wasu kyauttuka ga mutanen mazabarsa.

Daily Trust tace ‘dan majalisar mai wakiltar yankin Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano ya tallafa wa matasa da mata sama da 2000 a mazabar ta sa.

Alhassan Ado Doguwa ya kashe Naira miliyan 70 a kan mutanen da yake wakilta a majalisar tarayya.

Kyaututtukan da 'dan majalisar ya raba

Daga cikin kayan da aka raba wa al’ummar garuruwan Doguwa da Tudun Wada akwai kekunan dinki na wuta 500, da kuma kekunan dinki na kafa 500.

Read also

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Rahoton yace Honarabul Doguwa ya kuma raba tireloli hudu na takin zamani ga wasu zababbun manoma a karamar hukumar Tudun Wada da ke jihar Kano.

A cewar Doguwa wanda ya dade a majalisar wakilai na kasa, ya raba wadannan kyaututtuka ne domin ya gode wa mutanesa da suka zabe shi har sau shida.

‘Dan Majalisar Kano
Hon. Alhassan Ado Doguwa Hoto: hotpen.net
Source: UGC

Jawabin Hon. Alhassan Ado Doguwa

“Na zo nan ne domin in gode maku mutane na da kuka zabe ni sau shida, tun 1992.”
“Ina so in nuna godiya ta musamman gare ku. Mun zo domin mu talaffa wa mata da matasa 2000 kamar yadda na saba duk bayan kwana 35-40 a nan.” - Doguwa

Al’ummar Doguwa da kewaye sun gode wa ‘dan majalisar da wannan kudi da ya kawo a buhuna. Murtala Sule Garo yana cikin wadanda suka shaida rabon.

Read also

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na jihar Kano, Garo yace yana fata ba an yi wannan abin alheri ba ne da nufin daure wadanda suka karbi kayan.

Baya ga kekunan dinki da aka kawo, Alhassan Ado Doguwa ya kuma raba babura 500 ga matasa.

Rikicin APC

Kun ji cewa watakila Shugabannin APC su ladabta Sanatoci da Ministocin da wasu jiga-jigan jam'iyya da suka ja da Gwamnoni a zaben shugabanni da aka yi.

Wadanda suka saba wa zabin Gwamnoni a zabukan sun hada da Sanata Ibrahim Shekarau, Rochas Okorocha, Akinwumi Ambode, da Rauf Aregbesola.

Source: Legit

Online view pixel