Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

  • Wata kungiyar matasa a Arewa ta bayyana goyon baya ga Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023
  • Sun ce, ya kamata dukkan jam'iyyun siyasa su mara wa Tinubu baya su mika masa tikitin shugabancin kasa
  • Kungiyar ta bayyana haka ne duba da gogewar Bola Tinubu da sanin makamar aiki da hada kan Najeriya

Kano - Wata kungiyar Arewa mai suna Arewa Youth Alliance for 2023, ta bayyana goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Legas kuma Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa a 2023.

Kungiyar ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya da su fara shirin daukar Tinubu a matsayin dan takara daya tilo a Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Matasan yankin Arewa sun ce sun amince kowace jam'iyya ta mikawa Tinubu tikitin shugabanci a 2023
Jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

A cikin wata sanarwa da aka ba manema labarai a ranar Laraba a Kano ta hannun Ko’odinetan kungiyar, Hon Bello Lawan Bello, ya ce:

Read also

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

“Shugaban jam’iyyar APC yana da gogewa, sanin kasa da makamar aiki, dabarun gudanarwa na jagoranci da hada kan Najeriya bisa nasarorin da ya samu a matsayinsa na Gwamnan Legas kuma jagoran APC na kasa tare da ba da gudummawa mai yawa ga nasarar gwamnatin Buhari."

Abin da zai faru muddin APC ta hana Tinubu takarar Shugaban kasa – Tsohon Dan Majalisa

A watan Mayu ne, tsohon dan majalisar tarayya, Saheed Akinade-Fijabi, ya tabo batun wanda za a ba takara a jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Honarabul Saheed Akinade-Fijabi ya bayyana cewa za a samu bayyanar wata jam’iyya dabam, idan APC ba ta ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tikiti ba.

Saheed Akinade-Fijabi wanda ya taba wakiltar yankin jihar Oyo a majalisar tarayya, yana ganin za a iya samun matsala idan Jigon APC bai samu takara ba.

Read also

2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa

A ganin Akinade-Fijabi, wata jam’iyya ta dabam za ta bullo, ta doke APC da PDP mai adawa, idan APC ba ta tsaida tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ba.

Tsohon ‘dan majalisar ya na ganin wannan jam’iyya da za ta fito, za ta taimaka wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen ganin burinsa na yin mulki, ya tabbata.

Punch ta ce Fijabi ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan rediyo a Ibadan.

APC da PDP ba za su taba sauyawa ba: Jega ya bayyana matsalolin APC da PDP

A wani labarin, Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi zargin cewa jakunkunan kudi da ubannin gida sun mamaye manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya kuma rashin dimokradiyyar cikin gida a cikin jam’iyyun na iya haifar musu da rudani.

Jam'iyyar PDP da ta APC sune manyan jam'iyyun Najeriya, kamar yadda da yawa kowa ya sani.

Read also

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Jega, wanda ya yi magana ne a wani shirin talabijin a Legas, jiya, ya ce ba zai yiwu APC da PDP su canza su yi abin da ya dace ba kamar yadda ya bayyana a cikin fitinar taron gangamin da suka gudanar kwanan nan, Daily Sun ta ruwaito.

Source: Legit

Online view pixel