Yar majalisar dattijai ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC, Ta bayyana dalilai

Yar majalisar dattijai ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC, Ta bayyana dalilai

  • Yar majalisar dattijai daga jihar Anambra, Stella Oduah, ta sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a hukumance
  • A wurin taron da aka shirya mata, Oduah, ta bayyana cewa duk wanda ya kushe gwamnatin shugaba Buhari to ba shi da godiyar Allah
  • A cewarta Buhari ya kawo ayyukan raya ƙasa zuwa yankin kudu maso gabas, kuma kowane ɗan yankin ya san da haka

Anambra - Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa a majalisar dattijai, Sanata Stella Oduah, tace, "Duk wanda yace Buhari ya watsar da Kudu-Gabas, to baiwa kan shi adalci ba haka yankinsa."

Oduah, bisa wakilcin Amaka Ononuju, ta faɗi haka ne a wurin taron sauya sheƙarta da ya gudana a sakateriyar APC dake Awka, baban birnin Anambra, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

A cewar sanatan, ta ɗauki matakin ficewa daga PDP zuwa APC ne domin ta samu damar kawo dumbin ayyuka mazaɓarta daga gwamnatin tarayya.

Sanata Stella Oduah
Yar majalisar dattijai ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC, Ta bayyana dalilai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sanatan ta ƙara da cewa a lokacin da take cikin jam'iyyar hamayya, ba ta samu damar kawo cigaba da dama ga Al'ummar mazaɓarta ba.

A jawabinta tace:

"Babu adalci mutum yace shugaba Buhari da jam'iyyar APC ba su yi komai a yankin kudu maso gabas ba, wannan son rai ne."

Oduah ta yaba wa shugaban ƙasa Buhari

Hakanan kuma sanata Oduah ta yaba wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bisa, "manyan ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta yi a yankin kudu-gabas."

Bugu da ƙari tace babu bukatar ƙarin bayanai kan manyan ayyukan da gwamnatin APC ƙarƙashin shugaba Buhari ta yi a yankin kudu maso gabas domin kowa na gani.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Zaben jihar Anambra dake tafe

Sanatan ta bayyana cewa kasancewar yanzun ta dawo jam'iyya mai mulki, zata maida hankali wajen ɗaukar matakan da suka dace na cigaban ƙasa.

Oduah ta yi alƙawarin marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, Andy Ubah, baya a zaɓen gwamnan jihar Anambra dake tafe.

Tace zata yi iyakar bakin kokarinta wajen kawo kuri'u masu ɗumbin yawa ga jam'iyyar APC daga mazaɓarta.

A wani labarin kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abuɓakar, ya bayyana cewa yan Najeriya ne zasu baiwa PDP nasara a 2023

Atiku yace a halin yanzu mutane basu da wani zaɓi da ya wuce su sake amincewa da PDP a babban zaɓen 2023.

A ranar Asabar ne, PDP ta gudanar da gangamin tarukanta a matakin jihohi domin zaɓen shugabanninta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel