A karshe PDP ta bukaci Kotu ta tsige Gwamnan Zamfara da duk wadanda suka koma APC

A karshe PDP ta bukaci Kotu ta tsige Gwamnan Zamfara da duk wadanda suka koma APC

  • Jam’iyyar PDP ta shigar da kara a kan dambawar siyasar Zamfara a kotun tarayya
  • Lauyan PDP na so Alkali ya tsige Gwamna da sauran ‘Yan Majalisar jihar Zamfara
  • O.J. Onoja ya roki Mai shari’a Inyang Ekwo ya sauke duk wadanda suka koma APC

Abuja - A ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, 2021, jam’iyyar PDP ta kai kara, tana so a sauke masu rike da mukamai a jihar Zamfara da suka sauya-sheka.

Jaridar Punch tace jam’iyyar hammayar tana so a tsige gwamna Bello Matawalle, duka Sanatocin jihar uku da kuma ‘yan majalisa 30 da suka shiga jirgin APC.

Babban lauyan da ya tsaya wa PDP, O.J. Onoja, SAN ya shigar da kara a babban kotun tarayya na garin Abuja mai lamba FHC/ABJ/CS/650/2021 tun a Satumba.

O.J. Onoja ya bukaci Alkali mai shari’a Inyang Ekwo ya sauke Matawalle, Sanatocin Zamfara, ‘yan majalisar tarayya shida da na dokoki 24 da suka bar PDP.

Kara karanta wannan

Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 a kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

PDP tana so kotu ta raba gardama

A karar da lauyan PDP suka shigar, sun nemi kotu tayi fashin baki a kan sassan (2), 188, 287, 221, 177(c), 106(d) and 65(2)(b) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Lauyan da PDP ta dauko haya yana so kotu ta tantance cewa ko Matawalle da ‘yan majalisar jihar za su iya cigaba da rike mukamansu tun da sun sauya-sheka.

Da aka zauna a kotu, Onoja ya nemi Alkali ya bada dama a fara shirye-shiryen tunbuke Matawalle.

'Yan APC
Manyan APC a Zamfara Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Manyan lauyoyi sun gwabza a kotu

An samu sabani tsakanin lauyan PDP, Onoja da Lauyan da yake kare bangaren gwamnati, Mike Ozekhome, SAN a lokacin da aka zauna a kotun na tarayya.

Ozekhome yace lauyan jam’iyyar PDP bai bada isasshen lokaci da za a duba rokon da ya kawo ba. Babban lauyan ya bukaci a ba shi lokaci sosai ya yi nazari.

Kara karanta wannan

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

Alkali ya daga wannan shari’a zuwa ranar 2 ga watan Nuwamban 2021, domin a ji ko za a iya cusa mataimakin gwamnan Zamfara, Mahadi Gusau a karar.

PDP ta yi karar INEC, Lawan, Gbajabiamilla, Matawalle, dsr

Kafin nan jam’iyyar PDP mai hamayya ta yi karar hukumar zabe na kasa, INEC, shugabannin majalisar Najeriya, Matawalle da Alkalin Alkalan Zamfara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadannan ‘yan siyasa sun yi watsi da jam’iyyar PDP, sun koma APC bayan sun dare kan mulki a sakamakon hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel