Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

  • 'Socio-Economic Rights and Accountability Project' ta na karar Gwamnatin Najeriya
  • Kungiyar ta shiga kotun ne a kan shirin da ake yi na sa ido a kan wayoyin al’umma
  • SERAP tace yunkurin da ake yi ya ci karo da dokar kasa, kuma an keta alfarmar sirri

Abuja - Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta shigar da karar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu.

Wannan kungiya mai kare hakkin al’umma ta garzaya kotu ne a kan abin da ta kira haramtaccen yunkurin sa ido da za a rika yi a kan manhajar WhatsApp.

Jaridar Premium Times tace har ila gwamnatin tarayya za ta rika bibiyar wayoyi da sakonnin da mutane suke aika wa, har an ware N4.87bn domin wannan.

Kungiyar tace wannan yunkuri da gwamnatin kasar take yi ya saba doka, an shiga sirrin Bayin Allah.

Kara karanta wannan

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

Rokon Socio-Economic Rights and Accountability Project a kotu

A karar da SERAP ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1240/2021 a babban kotun tarayya na Abuja, ta bukaci a dakatar da hukumomi daga yin wannan aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace SERAP tana so kotu ta ayyana bibiyar waya da sakonni da kafar WhatsApp a matsayin abin da ya saba sassa na 37 da 39 da tsarin mulki.

Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Haka zalika tace sashe na 8 na kundin hakkin jama’a na kasashen Afrika da sassa na 17 da 19 na kundin kare hakkin mutane a Duniya ba su yarda da sa idon ba.

“Shirin bibiyar sakonnin WhatsApp, wayoyi da sakonnin salula da gwamnati take yi ya ci karo da tsare sirrin mutane da na iyalansu, da na gidajensu.”
“Gwamnati tana da nauyi a kan ta na kare mutanen Najeriya, da hana a keta alfarmarsu. Bibiyar wayoyinsu zai sa a rika sa masu idanu.” – SERAP.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

A cewar SERAP, babu wani dalili ko wata larurar da za ta sa a bi diddikin sirrin wayoyin mutane. Vanguard tace ba a sa ranar da za a soma wannan shari’ar ba.

Kolawole Oluwadare da Kehinde Oyewumi ne lauyoyin da suka tsaya wa SERAP. Abubakar Malami da Zainab Ahmed suna cikin wadanda za ayi shari’ar da su.

Tunde Bakare ya sake zuwa Aso Rock

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ku ka ji Tunde Bakare ya ziyarci Aso Villa, bayan ya fito yake cewa bangaren da shugaban kasa ya fito bai da wani tasirin kirki.

Bakare yace da haka ne da babu inda ya kai Arewa arziki domin sun dade a mulki. Haka zalika Faston ya bada misali da yadda Cif Obasanjo ya karya jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel