PDP ta dumfari Kotun koli, ta roki a tsige Gwamna, ‘Yan Majalisun Zamfara da suka koma APC

PDP ta dumfari Kotun koli, ta roki a tsige Gwamna, ‘Yan Majalisun Zamfara da suka koma APC

  • PDP ta shigar da karar wadanda su ka koma jam’iyyar APC a jihar Zamfara
  • Jam’iyyar adawar ta na so Alkali ya karbe kujerar duk wanda ya sauya-sheka
  • Idan PDP ta yi nasara, APC za ta iya rasa Gwamna da ‘Yan Majalisu da dama

This Day ta ce babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta fara kokarin sake karbe jihar Zamfara daga hannun mai girma gwamna Bello Matawalle.

Jam’iyyar PDP na kuma yunkurin karbe kujerun ‘yan majalisar dokoki na jiha, da ‘yan majalisar wakilan tarayya da sanatocin da suka koma APC.

PDP ta shigar da kara a wani babban kotun tarayya da ke Abuja, ta na so a tsige gwamnan Zamfara.

KU KARANTA: Yari ya ce masu neman Mataimakin Shugaban kasa a 2023 su na yaki da shi

Lauyoyi za su nemi su karbowa PDP kujerun Zamfara

Kamar yadda jaridar ta rahoto, mutum kusan 40 ake tuhuma a karar da jam’iyyar adawar ta kai ta hannun babban sakatarenta na kasa, Sanata Umar Tsuari.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC

Babban lauyan da ya tsaya wa PDP, Emmanuel Ukala SAN, ya hada da shugabannin majalisar tarayya, Ahmad Lawan; Femi Gbajabiamila a wannan shari’a.

Har ila yau, E Ukala SAN ya bukaci babban Alkalin jihar Zamfara, da shugaban majalisar dokokin jihar, da jam’iyyar APC da kuma INEC su kare kansu a kotu.

Sauran lauyoyin da PDP ta dauko haya sun hada da Edward Obiokor, M.S. Agwu, Miss O.J. Iheko, Dike Udenna, Okechukwu Omeodu da Reginald WB Nnwoka.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta kammala shirin zuwa kotu da Matawalle

Bello Matawalle da Muhammadu Buhari
Bello Matawalle da Muhammadu Buhari Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

A wannan kara da lauyoyin suka shigar, sun bukaci kotu ta ayyana cewa duk wani mai rike da mukami da ya sauya-sheka a jihar Zamfara, ya rasa kujerarsa.

Rahoton ya ce jam’iyyar ta nemi ayi shari’ar cikin gaggawa, a fitar da hukunci nan da kwanaki 30.

Masu rike da kujerar gwamnati da su ka koma APC a Zamfara

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

‘Yan majalisar dokokin da su ka bar PDP a jihar Zamfara sun hada da; Hon. Zaharadeen M. Sada, Hon. Anas Sarkin Fada, Hon. Nura Dahiru, Hon. Nasiru Mu’azu, Hon. Musa Bawa Musa, Hon. Aliyu Namaigora, Hon. Ibrahim Mohammed Naidda, Hon. Shafiu Dama, Hon. Kabiru Magaji, Hon. Nasiru Bello Lawal, Hon. Yusuf Alhassan Muhammad, Hon. Yusuf Muhammad, Hon. Shamsudeen Hassan, Hon. Aminu Yusuf Jangebe, Hon. Tukur Jekada B/Tudu, Hon. Faruk Musa Dosara, Hon. Nasiru Atiku, Hon. Abdulnasir Ibrahim, Hon. Mansur Mohammed, Hon. Ibrahim Mohammed Bukkuyum, Hon. Sani Dahiru.

Sannan kuma ‘yan majalisar wakilan tarayyar da suka bar PDP sun hada da; Hon. Shehu Ahmad, Hon. Bello Hassan Shinkafi, Hon. Ahmad Muhammad Bakura, Hon. Sani Umar D’Galadima, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, Hon. Kabiru Amadu Gusau.

Sanatoci sun hada da; Sahabi Alhaji Ya’u, Hassan Muhammad Nasiha, Lawal Hassan. Dukkaninsu, sun bi Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel