Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP

Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta samu koma baya a jihar Delta, inda wasu manyan jiga-jigai suka fice tare da ɗumbin masoyansu
  • Daga cikinsu har da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Monday Igbuya, da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya
  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tuni ta kammala shirin tarban manyan mutanen a watan Oktoba

Delta - Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Monday Igbuya, da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Chief Hon Solomon Edoja, sun fice daga jam'iyyar APC.

Punch ta rahoto cewa jiga-jigan siyasar na kan hanyarsu ta komawa babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Shugaban PDP reshen jihar Delta, Kingsley Esiso, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta hannun kakakin jam'iyyar, Latimore Oghenesivbe.

Kara karanta wannan

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Jam'iyyar PDP
Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP Hoto: informationng.com
Asali: UGC

A cewarsa tuni PDP ta shirya babban taro a filin Sapele Township ranar 23 ga watan Oktoba domin karɓar masu sauya shekan da ɗaruruwan magoya bayansu.

Gwamnan Delta zai tarbi masu sauya shekan

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shi ake tsammanin zai tarbi manyan mutanen a wurin taron.

A cewar sanarwar da PDP ta fitar, shugaban jam'iyya na Delta ta tsakiya, Chief F. Fovie, mambobinsa da haɗin guiwar shugaba na jiha, sun kammala duk wani shiri na gudanar da taron.

Wani sashin sanarwar yace:

"Wannan gangamin taron na cikin shirye-shiryen da muka shirya domin nuna cewa a siyasar Delta babu kamar PDP."
"Kuma itace kaɗai jam'iyyar da aka gina ta da kyakkyawar alaƙa da mutanen jihar Delta, yayin da muke fuskantar babban zaɓen 2023."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

A wani labarin kuma kun ji cewa Manyan makusantan Gwamna sun sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya PDP

Manyan nakusa da gwamnan Anambra, Willie Obiano, guda 5 sun sauya sheka daga APGA zuwa jam'iyyar PDP.

Mutanen sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda gazawar gwamnatin APGA da kuma rashin adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel