Manyan makusantan Gwamna sun sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya PDP

Manyan makusantan Gwamna sun sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya PDP

  • Manyan nakusa da gwamnan Anambra, Willie Obiano, guda 5 sun sauya sheka daga APGA zuwa jam'iyyar PDP
  • Mutanen sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda gazawar gwamnatin APGA da kuma rashin adalci
  • Sauran waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da shugaban matasan jam'iyyar AGPA, masu taimakawa na musamman da kansiloli

Anambra - Mutum biyar daga cikin mataimakan gwamnan Anambra, Willie Obiano, sun fice daga jam'iyyar APGA, sun koma PDP, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Bayan ficewarsu daga APGA zuwa PDP, waɗanda suka sauya shekan sun sha alwashin tallafawa ɗan takarar gwamna, Valentine Ozigbo, domin ya samu nasara a zaɓen dake tafe.

Gwamna Obiano na jihar Anambra
Manyan makusantan Gwamna sun sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Meyasa suka fice daga jam'iyyar APGA?

Jiga-jigan jam'iyyar APGA da suka sauya sheka zuwa PDP bisa jagorancin shugaban matasa, Eziokwu Magnus, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda gazawar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

A cewarsu gwamnatin yanzun ƙarƙashin jagorancin Jam'iyyar APGA ta gaza yin kataɓus ga kuma rashin adalci da yayi mata katutu.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an gudanar da bikin karɓar waɗanda suka sauya shekar ne a gidan gwamnatin jihar Delta dake Asaba, ranar Talata da daddare.

Su waye mutum 5 da suka guji gwamna?

Magnus ya koma PDP ne tare da babban mai taimakawa gwamna a ɓangaren muhalli, Abuchi Egboo, mai taimakawa gwamna ta ɓangaren ɗaukar matakin doka, Barista Eziafa Charisma.

Sauran kuma sun haɗa da, mai taimakawa ta ɓangaren ayyuka, Engr Ibik Kelvin, mai taimakawa a ɓangaren sadarwa, Emeka Nwabunwane, shugaban matasan Anambra ta tsakiya da sauransu.

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel