Rikicin APC: Buni, gwamnan CBN da Malami sun garzaya Landan, Za su gana da shugaba Buhari

Rikicin APC: Buni, gwamnan CBN da Malami sun garzaya Landan, Za su gana da shugaba Buhari

  • Yayin da APC ta tsunduma cikin rikicin shugabanci, gwamna Buni, Malami da gwamnan CBN sun nufi Landan wurin Buhari
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Mala Buni mai barin gado ya canza tunani, daga Dubai duba lafiya zai wuce Landan ya gana da Buhari
  • Rahoto ya nuna cewa Buni zai gana da Buhari ne domin jin abinda ke faruwa daga bakinsa kan zancen tsige shi

Shugaban jam'iyyar APC mai barin gado, Gwamna Mai Mala Buni, ya dira Landan domin gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Wata majiya ta ce gwamna Buni da ake tsammanin zai dawo Najeriya ranar Laraba daga haɗaɗɗiyar daular Larabawa, ya canza tunani.

Buni zai gana da Buhari a Landan
Rikicin APC: Buni, gwamnan CBN da Malami sun garzaya Landan, Za su gana da shugaba Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa ya tafi Dubai ne domin duba lafiyarsa, yayin da rikicin APC ya ɗauki wani sabon salo bayan barinsa.

Kara karanta wannan

Wajibi APC ta fita tsara a cikin jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin shugabancin APC

Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yanzun zai nufi Landan domin gana wa da shugaban ƙasa Buhari kan halin da jam'iyya ta tsinci kanta."

Haka nan kuma, rahoto ya nuna cewa tuni Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya dira birnin Landan don gana wa da Buhari.

Wani babban jigon gwamnatin tarayya da ake ganin zai gana da Buhari a Landan bayan Malami da Buni, shi ne gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Sai dai babu wani tabbacin cewa gwamnan CBN ɗin ya ɗira babban birnin Burtaniya a jiya da daddare.

Gabanin tafiyarsa Landan, wata takarda ta bayyana kuma ta musanta ikirarin gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, game da yadda aka tsige Buni daga shugaban APC na rikon kwarya.

Rikicin APC ya koma Landan

Wata majiya kuma cikin kwarin guiwa ta kara da cewa rikicin APC ya koma birnin Landan yayin da gwamna Buni ke kokarin tsira daga lamarin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

"Maimakon dawowa gida, Buni ya tafi Landan domin bayyana matsayarsa kuma ya ji daga bakin Buhari kan cewa shi ya bada umarnin tsige shi ko kuma ba haka bane."
"Ya tafi Landan da duk abubuwan da suka faru a cikin jam'iyya. Ya jaddada cewa Buhari bai faɗa masa da baki ko aike masa a rubuce ba kuma ba zai dogara da abubuwan dake faruwa ba, yana son ji daga bakin Buhari."

A wani labarin na daban kuma Kotu zata fara zama kan bukatar FG na mika Abba Kyari kasar Amurka

Kotun tarayya dake zaune a Abuja ta sanya ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara zaman duba bukatar mika Abba Kyari Amurka.

Gwamnatin Najeriya ta nemi sahalewar Kotu a wani bangare na amincewarta da bukatar mika Kyari ga kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel