Wajibi APC ta banbanta da sauran jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin APC

Wajibi APC ta banbanta da sauran jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin APC

  • Jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya zama wajibi APC ta fita tsara wajen tafiyar da harkokinta na cikin gida
  • Ɗan takarar shugaban ƙasan ya yaba wa Buhari kan nuna yaƙininsa a APC da kuma kokarin kare ta daga tarwatsewa
  • A cewar tsohon gwamnan Legas, shugaba Buhari ne ya jagoranci kafa APC da kuma shi, wajibi su kare manufofinta

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya ce ya zama wajibi jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta rinka kwatanta adalci wajen tafiyar da harkokinta.

The Cable ta rahoto ɗan takarar shugaban kasan na cewa jam'iyyar APC zata fi tasiri a ƙasar nan matuƙar ta na tafiyar da demokaraɗiyya a cikin gida.

Kalaman jagoran na ƙasa na zuwa ne yayin da rikicin shugabancin APC ke kara kamari, inda ake ganin Buni ya rasa kujerarsa ta shugaban kwamitin riko.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya faɗi yankin da Magajin Shugaba Buhari zai fito a 2023

Bola Tinubu
Wajibi APC ta banbanta da sauran jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu support group/facebook
Asali: Facebook

A sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, Bola Tinubu. ya yaba wa shugaban ƙasa Buhari bisa nuna damuwarsa da yakininsa ga jam'iyya mai mulki.

Tsohon gwamnan ya ce yayin da kowane mamba ke da damar neman kujerar siyasa, wajibi su tabbatar, "Akwai haɗin kai a zukatan su."

The Nation ta rahoto Ya ce:

"Kwanan nan shugaba Buhari ya yi wasu kalamai masu amfani game da karfi da kuma manufar jam'iyyar mu ta APC. Ya fahimci bukatar zaman lafiya a cikin gida domin cika manufofin cigaba da aka kafa ta kansu."
"Jam'iyyar mu ta zo ne domin ita ce amsar addu'ar neman gyara da mutane suka yi, su samu gwamnatin da zata kawo cigaba domin goben yan Najeriya ya yi kyau."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugabanta na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

Yadda aka kafa APC

Tinubu ya ƙara da cewa mafi yawan jagororin kawo cigaba sun zuba lokacin su, karfi, dabaru da kuɗeɗen su wajen kafa APC da nufin gyara fasalin Najeriya.

"Shugaban ƙasa shi ne tushen kafa APC, nima na taka rawa kaɗan. Dan haka a matsayin iyayen jam'iyyar dole mu kare manufofin da muka kafa ta a akai."

A wani labarin na daban kuma Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari

Wani mutumi ɗan asalin jihar Kano ya kuduri aniyar yin tattaki tun daga Abuja zuwa Legas domin nuna wa Tinubu ana tare.

Hussein Lawan ya ce zai yi wannan sadaukarwa ne a madadin matasa ya roki Tinubu ya fito takara don tallafawa matasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel