Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

  • Yayinda ake tsaka sharhi kan jawabin El-Rufa'i, hadiman Mai Mala Buni sun saki wata wasikar da sukace Buni ya turawa jam'iyyar
  • Gwamna Mai Mala yanzu dai an ce ana hadaddiyar daular larabawa UAE ganin Likita
  • Wannan na faruwa daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Landan shima ganin Likita

Rikicin da ya barke cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya dau sabon salo yayinda wata wasikar Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ke karyata jawabin Gwamna Nasir El-Rufa'i.

Wasikar ta karyata jawabin El-Rufa'i na cewa Shugaba Buhari ya bada umurnin tunbuke Mai Mala Buni, cewar TheNation.

Hadiman Mai Mala sun bayyana cewa maigidansa ba korarsa aka yi ba, da kansa ya mika mulkin jamiyyar hannun Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, kafin tafiya jinya kasar Dubai.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i
Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i Hoto: TheNation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashen wasikar mai dauke da kwanar watan 28 ga Febrairu tace:

"Ina mai sanar da kai cewa zan tafi neman lafiya kasar UAE daga Yau, 28 ga Febrairu, 2022."
"Saboda haka, na wakilta ayyukan ofishina na Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar nan gare ka."
"Ina kira ga mambobi su hada kai da Gwamna Abubakar Sani Bello ta hanyar bashi goyon baya kamar yadda kuka bani."

Wani hadimin Buni, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa TheNation cewa:

"Ba zai yiwu ace wani ko gungun gwamnoni sun cire Buni ba saboda wasikarsa a bayyana take. Ya bi ka'ida kuma ya ce Bello ya wakilcesa."
"Gwamna El-Rufa'i ya fadawa Najeriya gaskiyar abinda ya auku tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni ranar Lahadi. Akwai kura-kurai cikin maganarsa."

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin shugabancin APC

"Yan Najeriya su tambayi Bello da mambobin kwamitin rikon kwarya ko Buni ya basu wasika."

Jawabin El-Rufa'i

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kujerar Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan.

A hirar da yayi a shirin Politics Today, El-Rufa'i ya ce Buni ko ya dawo an fitittikeshi daga kujerar gaba daya har abada.

Ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC 19 sun yi ittifaki kan cire Mai Mala Buni.

El-Rufa'i yace:

"Buni ya tafi har abada, Sakatare ya tafi. Gwamna Bello ne kan kan kujerar yanzu kuma Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnoni 19 na bayansa. Buni ko ya dawo zai dawo ne a matsayin Gwamnan Yobe amma ba Shugaban jam'iyyarmu ba."
"Shugaba Buhari ya bada umurnin cireshi. Buni da mutanensa sun samu wata doka daga kotu na hana taron gangami amma ya boye."

Kara karanta wannan

Tsige Mala Buni: Gwamnoni 2 da Minista sun garzaya Landan, za su sa labule da Buhari

"Ban san dalilin da zai sa mutum yayi irin haka ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel