Matar 'Yar'adua da Jiga Jigan Najeriya Sun Hallara Abuja Auren 'Ya'yan Sanata Goje

Matar 'Yar'adua da Jiga Jigan Najeriya Sun Hallara Abuja Auren 'Ya'yan Sanata Goje

  • Manyan mata daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarci walimar bikin auren Dr Farida Danjuma Goje da Barista Na’ima Goje a Abuja
  • Malamai sun gabatar da nasihohi kan zaman lafiya da biyayya ga miji, suna tunasar da kyawawan halayen marigayiya Hajiya Yalwa Danjuma Goje
  • Tsohuwar 'yar majalisar wakilan tarayya, Hon. Aishatu Jibrin Dukku ta gode wa al’ummar da suka halarci taron walimar a madadin iyayen amare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Walimar bikin auren Dr Farida Goje da Barista Na’ima Goje ta samu halartar manyan mata daga ciki da wajen Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da walimar ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, 2025, a gidan Sanata Danjuma Goje a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Auren yar Goje
Manyan mutane sun halarci walimar auren 'ya'yan Sanata Goje. Hoto: Muhammad Adamu Yayari
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda aka gudanar a walimar ne a cikin wani sako da hadimin Sanata Goje a fannin yada labarai, Muhammad Adamu Yayari ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda suka halarci walimar akwai Hajiya Turai Umaru Musa Yar’adua, Hajiya Amina Namadi Sambo, Sanata Aishatu Dahiru Binani da sauransu.

Malamai irinsu Sheikh Adamu Muhammad Dokoro sun gabatar da nasihohi ga amare kan muhimmancin zaman aure.

Matan da suka halarci auren 'ya'yan Goje

Walimar ta janyo hankalin manyan mata kamar tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Hajiya Turai Yar’adua, tsohuwar ministan mata, Hajiya Zainab Maina, da Hajiya Amina Namadi Sambo.

Haka zalika, Hajiya Mairo Aminu Waziri Tambuwal da tsohuwar ministar mata Paulen Talen sun samu halarta.

Sauran mata masu fada a ji daga bangarori daban-daban na kasar nan sun halarci walimar wanda hakan ya kara armashi ga bikin.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sabunta katafaren masallaci, malamai da 'yan siyasa sun hallara

Malaman musulunci sun yi nasiha ga amare

Malamai da suka hada da Sheikh Adamu Muhammad Dokoro, Dr Umar Garba Dokaji da Sheikh Tahir Alyasin sun ja hankali kan muhimmancin biyayya ga miji da zaman lafiya a aure.

Sun yi kira ga amare suyi koyi da marigayiya Hajiya Yalwa Danjuma Goje, wadda ta yi suna wajen taimakon al’umma, addini da gudanar da rayuwa mai kyau.

Malamai sun bayyana cewa biyayya ga miji da tallafa wa addini zai sauƙaƙa wa mace shiga Aljanna.

Jawabin godiya ga mahalarta taron

Tsohuwar 'yar majalisa, Hon. Aishatu Jibrin Dukku ta gode wa al’ummar da suka halarci walimar auren a madadin iyayen amare, tana mai nuna farin cikin su ga jama'a.

A jawabin nata, ta ce,

“Muna godiya ga dukkan waɗanda suka halarci wannan walima mai albarka. Allah ya sanya wannan aure ya kasance mai albarka.”

- Hon. Aishatu Jibrin Dukku

Kara karanta wannan

Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron

An yi fatan alheri ga amare

An kammala walimar cikin farin ciki da addu’o’in fatan alheri ga amare. Mahalarta sun bayyana gamsuwarsu da yadda taron ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali.

Haka zalika an yi addu'o'in samun zaman lafiya ga amare da angwaye da fatan Allah ya ba su zuriya mai albarka.

Tawagar daurin aure ta yi hadari a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wani mummunan hadarin mota ya ritsa da wata tawagar daurin aure da suka taso daga Filato.

Rahotanni sun nuna cewa mutane 19 sun rasu cikin tawagar daurin auren kuma sun fito ne daga Filato domin komawa gida jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng