Babu Bahaushe Ko 1: Jerin Manyan Mawaka 10 Mafi Arziki a Nigeria a 2024

Babu Bahaushe Ko 1: Jerin Manyan Mawaka 10 Mafi Arziki a Nigeria a 2024

Allah ya albarkaci Nigeria da tarin mawakan da ake ji da su a duniya, wadanda kuma suka mallaki gidaje, motoci, jiragen sama da duk wani alatu na rayuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A Arewacin kasar, dole ne a saka sunan Dauda Kahutu Rarara, Nazifi Asnanic, Ali Jita, Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Umar M Sharif, Lilin Baba, a jerin mawaka masu kudi.

Sai dai duk da hakan, an nemi sunayensu a rasa a yayin da shafin Dockaysworld ya fitar da jadawalin mawaka 10 mafi arziki a Nigeria, a wannan shekarar ta 2024.

Jerin mawaka 10 mafi arziki a Najeriya.
An nemi Bahaushe an rasa a yayin da aka fitar da jerin mawaka 10 mafi arziki a Najeriya. Hoto: @davido, @rudeboypsquare, @wizkidayo
Asali: Twitter

A dawalin, sunayen mawakan Kudancin kasar ne kawai aka gani, abin da ya bar mu da tambayar 'ina mawakan Hausa suka makale?' amsar da za mu nemo ta nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bari mu yi nazarin mawaka mafi arziki a Nigeria a 2024:

1. Wizkid: Ya mallaki akalla N44.6bn

Wizkid shi ne mawaƙin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya wanda aka kiyasta cewa yana da kuɗin da ya kai sama da dala miliyan 30 (Naira biliyan 44.6) a shekarar 2024.

An ce ya mallaki wannan kudin ne daga wakokinsa da ya sayar a kasuwa, wasannin da ya ke hadawa, tallace-tallace da yake yi da kuma karbar jakadancin kamfanoni.

A yayin da miliyoyin mutane ke sauraron wakokinsa a kafofi irinsu spotify, an ce Wizkid yana samun kudin shiga mai yawa a kowane wata.

PM News ta ruwaito Wizkid ne kadai dan Najeriya na farko kuma daya tilo da ya sayar da tikitin shiga filin wasa na 02 Arena da ke kasar Ingila kwana uku a jere.

Kara karanta wannan

Naira ta koma gidan jiya, kudin Najeriya ya dawo mafi rashin daraja a duniya

2. P Square: Sun mallaki akalla N40.5bn

P-Square, (Peter Okoye (Mr.P) da Paul Okoye (Rudeboy), suna daga cikin manyan mawaka 10 na Nigeria bayan da suka mallaki jimlar dalar Amurka miliyan 27 (Naira biliyan 40.5).

Tagwayen mawakan suna samun kuɗi daga tallace-tallace, sayar da wakokinsu, yin wasanni, zama ambasada na kamfanoni da kuma tafiyar da nasu kamfanin.

Duk da sun mallaki kadarori da dama a Najeriya da kasashen ketare, P-Square sun sayi jirgin sama na alfarma na miliyoyin daloli a shekarar 2012, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

3. Davido: Ya mallaki akalla N37bn

David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, mawakin Najeriya ne wanda ke kan gaba a jerin manyan mawakan Najeriya da dukiyar da ta kai dala miliyan 25 (Naira biliyan 37).

Davido yana samun kudin shiga, daga tallace-tallace, kafofin sauraron wakoki, wasanni a kasashen waje, zama ambasada ga kamfanoni da sauran su.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Bayan sana'arsa ta waka, shi ne wanda ya kafa kamfanin waka na Davido Music Worldwide (DMW) wanda ke kawo mashi manyan kudade.

4. Don Jazzy: Ya mallaki akalla N35.6bn

Don Jazzy, wanda ainahin sunansa Micheal Ajereh Collins, shi ne na 4 mafi arziki a cikin mawakan Najeriya da dukiyar da ta kai dala miliyan 24 (Naira biliyan 35.6) a shekarar 2024.

Babbar hanyar samun kudin Don Jazzy a yanzu ita ce zamansa na wanda ya kafa kamfanin Mavin Records, mafi girma kuma mafi nasara a tarihin Najeriya tare da manyan mawaƙa kamar Rema, Ayra Starr, Crayon, da Johnny Drille.

Don Jazzy yana kuma samun kudin shiga daga kamfanonin sa na Mavin Energy da Jazzy's Burger wanda ya kaddamar a cikin 2013 da 2022.

Sauran hanyoyin samun kudin shigarsa sun hada da talla, da zama jakadan manyan kamfanoni kamar MTN, Loya Milk, Samsung, Konga, Glo, Hantec Market, da Quidax.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

5. Burna Boy: Ya mallaki akalla N32.7bn

Damian Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, mawakin Najeriya ne kuma marubucin waka wanda ya mallaki dukiyar da ta kai kimanin dalar Amurka miliyan 22 (Naira biliyan 32.7).

Yana daya daga cikin mawakan da suka fi karbar kudi idan aka zo batun gayyatarsa wasa, an sha sayar tikitin filayen wasa a Najeriya da sauran kasashen duniya idan zai yi wasa.

Baya ga aikinsa na waka, Burna Boy ya kuma rattaba hannu kan haɗin gwiwa da manyan kamfanoni, ciki har da Nike, Cîroc, da Apple Music, inda yake aiki a matsayin jakada.

Sauran mawaka 5 mafi arziki a Najeriya

6. Olamide - Ya mallaki $15m

7. 2Baba - Ya mallaki $13.5m

8. Phyno - Ya mallaki $12m

9. Tiwa Savage - Ta mallaki $10m

10. Timaya - Ya mallaki $9m

Davido zai rabawa marayu N300m

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya sanar da aniyarsa ta raba Naira miliyan 300 ga marayu.

Kara karanta wannan

Bambarakwai: Jerin kasashe 5 da mata ke biyan mazaje sadakin aure

Wannan dai a cewar Davido, na daga cikin gudunmawar da yake bayarwa duk shekara, inda wanna karon zai raba kudin ga gidajen marayu da ke a fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel