Bidiyo: Mawaƙi Wizkid ya kafa tarihi, ya raƙashe a wani bikin chasu a Saudi Arabia

Bidiyo: Mawaƙi Wizkid ya kafa tarihi, ya raƙashe a wani bikin chasu a Saudi Arabia

  • Sannane mawakin Najeriya da yayi shuhura a duniya, Wizkid, ya baje-kolinsa a wani bikin shagalin wasanni a kasar Saudi Arabia
  • Mawakin ya halarci bikin chasun da aka yi a NXT LVL Arena a birnin Riyadh inda ya rakashe tare da dubban jama'a da suka samu zuwa
  • Tare da taimakon DJ Tunez da tawagarsa, ya gwangwaje su da wakokinsa masu ratsa zuciya kamar su Essence, Ojuelegba, Joro, Come Closer da sauransu

Fitaccen mawakin zamani, Wizkid, ya kafa sabon tarihi a duniya inda ya zama mawakin farko da ya hau kanun labarai a wani chasu da aka shirya a Saudi Arabia.

Ana shagalin ne a NXT LVL Arena dake Riyadh Boulevard a kasar Saudi Arabia, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

Mawaki Wizkid
Mawaƙi Wizkid ya kafa tarihi, ya raƙashe a wani bikin chasu a Saudi Arabia. Hoto daga thewhistler.ng
Asali: UGC

Mawakin da ya samu lambobin yabo kuma marubucin wakoki ya girgije tare da rakashewa a gaban dubban jama'a a daren Alhamis, 4 ga watan Augustan 2022.

Mawakin tare da taimakon DJ Tunez da tawagarsa ta makada sun birge jama'a da irin sautinsu inda suka saki sabbin da tsofaffin wakokinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bai yi kasa a guiwa ba, ya dage inda ya rakashe da wakokinsa kamar: Essence, Ojuelegba, Joro, Come Closer, Beat of Life, Mood, Ginger, Soco da sauransu.

Bikin da ake yi a tsakiyar gabas din ana bayyana shi da gagarumin bikin wasanni na duniya inda ake gasa tare da nishadantarwa da kuma bayyana al'adu.

An fara a ranar 14 ga watan Yuli kuma za a kammala zuwa ranar 8 ga watan Satumba.

Bikin mai suna Gamer8 ya kawo shirye-shirye, raye-raye da kida a duniyar wasanni ga masoyan hakan.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Wannan rakashewar da yayi a bikin ya zo ne bayan makonni kadan da aka sanar da cewa zai halarci wani shagalin Rolling Loud a Miami dake New York.

Wizkid zai girgije a bikin tare da sauran taurarin duniya a watan Satumba.

Hotuna da bidiyo: Jaruma Nafisa Abdullahi zata kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata

A wani labari na daban, fitacciyar jarumar masana'antar Kannywood kuma 'yar kasuwa, Nafisat Abdullahi, za ta kaddamar da katafaren kamfanin yin jakunkuna mata.

Jarumar ta wallafar sanarwar a shafinta na Instagram inda yake biye da bidiyo da hotunan jakunkunan mata 'yan kwalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel