Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa

Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa

- Mawakin nan dan Najeriya, Peter Okoye wanda aka fi sani da Mr P na Psquare, ya wallafa hotunan kayatattun motocinsa

- A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram ya bayyana galla-gallan motocinsa guda 6

- Ya yi wallafar ne a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2021, inda aka gan shi a tsaye da faffadan kirjinsa mai burgewa

Wannan mawakin dan Najeriya, Peter Okoye wanda aka fi sani da Mr P na Psquare ya wallafa bidiyon tsadaddun motocinsa a shafinsa na Instagram.

A wani guntun bidiyo da ya wallafa a shafinsa a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2021, yana tsaye da alamun dukiya ta tsaya masa.

Ya wallafa yadda garejin motocinsa da yake cikin kasaitaccen gidansa yake makil da wasu manyan motoci masu burgewa, The Nation ta wallafa.

Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa
Bidiyon kasaitattun motoci 6 da mawaki Peter Okoye ya mallaka sun gigita masoyansa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa

Kamar yadda ya wallafa; "Ya kuke? Ya rayuwarku? Ya ranakun karshen makonku? Wannan shine Mr. P, inda kirjin cikakken namiji da motoci 6. Ku duba ku gani".

A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel