Jami’an tsaron fararen kaya sun aikawa D’ Jazzy da Tiwa Savage goron gayyata kwanaki

Jami’an tsaron fararen kaya sun aikawa D’ Jazzy da Tiwa Savage goron gayyata kwanaki

- DSS sun yi wa Tiwa Savage da Don Jazzy tambayoyi a ofishinsu na Legas

- Jami’an tsaron sun gargadi Mawakan su san irin abin da za su rika fada

- Hukuma ta na jan-kunne a kan yin abin da zai iya batawa gwamnati rai

Tauraron mawakin nan kuma mai shirya wasa, Don Jazzy da fitacciyyar mawakiya Tiwa Savage sun amsa gayyatar da jami’an tsaron DSS su ka yi masu.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020 cewa DSS sun ja-kunnen Don Jazzy da Tiwa Savage a kan sukar gwamnati.

Mawakiya Tiwa Savage ta fada hannun DSS ne a sakamakon korafin ‘WeAreTired’ da ta rika yi a watan Agusta game da yawan fyade da ake yi a Najeriya.

A jeringiyar sakonnin da taurariyar ta rika aikawa a shafinta na Twitter, ta jawo hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yawan aukuwar fyade.

KU KARANTA: D' Jazzy da Tiwa Savage su na cikin mawaka masu farin jini

Jami’an tsaron fararen kaya sun aikawa D’ Jazzy da Tiwa Savage goron gayyata kwanaki
Shugaban DSS na kasa tare da Shugaba Buhari
Asali: Twitter

Savage da Don Jazzy sun ziyarci ofishin DSS da ke garin Legas, inda aka gargade su game da irin maganganun da ya kamata su rika yi a dandalin sada zumunta.

Jaridar ta ce tun daga lokacin da Don Jazzy da Tiwa Savage su ka fada hannun DSS, ba su cigaba da babatu a kafofin sadarwa na zamani kamar yadda su ka saba ba.

Rahoton ya ce an yi wannan ganawa da mawakan ne a ofishin DSS da ke Shangisha a watan Agusta.

Miss Savage ta yi watsi da gwagwarmayar ‘WeAreTired’ da ta ke yi a shafinta. Shi kuma Don Jazzy ya rage huldar da ya ke yi a shafin Twitter a halin yanzu.

Shi ma kwamishinan ‘yan sanda na Legas, ya gayyaci Yemi Alade da Waje, inda ya nemi su guji kalaman siyasar da za su iya jawo fushin shugaba Muhammadu Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel