Davido ya tashi da fiye da Naira Biliyan 10 ($22m) a cikin watanni 12 a shekarar 2021

Davido ya tashi da fiye da Naira Biliyan 10 ($22m) a cikin watanni 12 a shekarar 2021

  • David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya yi ikirarin ya samu Dala miliyan 22.3 a shekarar 2021
  • Mawakin ya bayyana hakan ne da yake magana a shafin Instagram, yace wani aikin sai a 2022
  • Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, abin da Tauraron ya samu a bara sun kusa kai Naira biliyan 10

David Adeleke, babban mawakin Najeriya wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana irin kudin da ya samu a shekarar da ta gabata.

Da yake magana a shafinsa na sada zumunta na Instagram a jiya, Davido yace ya samu Dala fam miliyan 22.3 a shekarar nan (2021).

Mawakin ya yi wannan magana ne a ranar 31 ga watan Disamba, 2021, ya na mai sa ran wannan shekara ta 2022 ta fi kawo alheri.

Kara karanta wannan

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

“2022 za azurta dangi. Na samu Dala miliyan 22.3 a shekarar nan.” - Davido.

Kamar yadda Pulse ta fitar da rahoto, a karshe attajirin ya kare maganar ta sa da ashar.

Davido
Mawakin Duniya, Davido Hoto: @Davido
Asali: Instagram

An ja kaya inji Asa Asika

Manajan mawakin, Asa Asika ya tabbatar da wannan ikirari da Davido ya yi, yace babu shakka sun samu kudi masu yawa a bana.

“An ji dadi a shekarar 2021, mun samu kudi sosai @davido.” - Asa Asika

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shakka babu, Davido ya na cikin manyan attajiran taurarin da ake ji da su a kasar nan.

Mawakin ya samu kudi sosai daga wake-wakensa da kuma tallar da yake yi wa manyan kamfanoni a shekarar da ta wuce.

A karshen shekarar ne ya samu wata kwangilar talla da kamfanin Puma, ana sa ran zai samu daloli sosai daga yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Babu yadda za a yi in sake talauci a duniya, In ji shahararren mawaƙi, Timaya

Tauraron ya nuna irin arzikinsa a shekarar nan da ya saye wata katuwar mota wanda shigo da ita kurum sai kasurgumin attijiri.

An hadawa Davido kudi

David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu Naira miliyan 200 daga hannun masoyansa da ya cika shekara 28 a Duniya.

A karshe Davido ya tattara wadannan kudi, ya kara da Naira miliyan 50 domin a rabawa marayu da sauran mabukata a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel