Jerin Sunayen Attajiran Najeriya 40 da Suka Mallaki Jiragen Sama Na Alfarma da Yawan Kudadensu

Jerin Sunayen Attajiran Najeriya 40 da Suka Mallaki Jiragen Sama Na Alfarma da Yawan Kudadensu

A Najeriya, mallakar jirgin sama ba karamin abu ba ne a kasar wanda hakan ke nuna girman mutum a cikin al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Mafi yawan 'yan kasar da suka mallaki jiragen sun hada da 'yan siyasa da Fasto da kuma mawaka sun mallaki jiragen sama, cewar Ambusinessng.

Jerin wadanda suka mallaki jiragen sama na alfarma a Najeriya
Attajiran Najeriya da suka mallaki jiragen sama. Hoto: Dangote Group, Raymart Aviation.
Asali: UGC

Jerin attajiran da suka mallaki jiragen sama

Kamar yadda AMB ta tattaro kula da jirgin sama a shekara ya na iya cin kudi har naira miliyan 290 zuwa 580, cewar SolaceBase..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen attajiran da suka mallaki jirgi a Najeriya da kuma yawan kudadensu.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan kwamitin mutum 36 da za suyi aikin kara albashin ma'aikata

1. Aliko Dangote – Shugaban kamfanin Dangote group (Dala biliyan 19.6)

2. Mike Adenuga – Shugaban kamfanin Globacom (Dala biliyan 7)

3. Allen Onyema – Mammallakin Airpeace (Dala biliyan 3.1)

4. Arthur Eze – Shugaban kamfanin Atlas Oranto (Dala biliyan 5.8)

5. Igho Sanomi – dan kasuwa (dala biliyan 1)

6. Adedeji Adeleke - Shugaban Jami'ar Adeleke (dala miliyan 700)

7. Cletus Madubugwu Ibeto – Shugaban Ibeto (dala biliyan 3.8)

8. Apostle Johnson Suleman – Fasto (dala miliyan 10.5)

9. Dakta Bryant Orjiako – Shugaban kamfanin SEPLAT (dala biliyan 1.2)

10. Femi Otedola – dan kasuwa (dala biliyan 1.2)

11. Orji Uzor Kalu – dan siyasa (dala biliyan 1.1)

12. Shugaba Bola Tinubu – Dan kasuwa (dala biliyan 8.4)

13. Fasto David Oyedepo – Fasto (dala miliyan 200)

14. Joseph Arumemi-Ikhide – shugaban Arik Air (dala biliyan 3)

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 17, 000 a Karkashin Buhari da Tinubu

15. Theophilus Danjuma – dan siyasa (dala biliyan 1.1)

16. Fasto Adeboye – Fasto (dala miliyan 65)

17. Fasto Ayo Oritsejafor – Fasto (dala miliyan 32)

18. Folorunsho Alakija – 'Yar kasuwa (dala biliyan 1.53)

19. Ibrahim Badamasi Babangida – tsohon shugaban kasa – dala biliyan 5

20. Atiku Abubakar – dan siyasa (dala biliyan 1.8)

21. Olusegun Obasanjo – dan siyasa (dala biliyan1.6)

22. Rochas Okorocha – dan siyasa (dala biliyan 1.4)

23. Rotimi Amaechi – dan siyasa (dala miliyan 780)

24. Senator Ali Modu Sheriff – dan siyasa (dala miliyan 1 zuwa miliyan 5)

25.Godswill Akpabio – dan siyasa (dala miliyan 20)

26. Obi Cubana – Dan kasuwa (dala miliyan 96)

27. Tiwa Savage – mawakiya (dala miliyan 17)

28. Phyno – mawaki (dala miliyan 12)

29. Ned Nwoko – Dan kasuwa (dala biliyan 1.2)

Kara karanta wannan

Atiku ya jefawa Gwamnatin Tinubu zafafan tambayoyi 5 kan bashin $3.3bn da aka ci

30. Fasto Chris Oyakhilome – (dala miliyan 50)

31. Fasto Jeremiah Omoto Funfeyin – (dala miliyan 35)

32. Wizkid – mawaki (dala miliyan 30)

33. Don Jazzy – mawaki (dala miliyan 10)

34. Patrick Ifeanyi Ubah – dan siyasa (dala biliyan 1.7)

35. Jimoh Ibrahim – dan kasuwa (dala biliyan 1.1)

36. DJ Cuppy – (dala miliyan 3)

37. Ernest Azudialu Obiejesi – dan kasuwa (dala miliyan 900)

38. Olamide – mawaki (dala miliyan 12)

39. P-Square – mawaki – (dala miliyan 100)

40. Jide Omokore - babu cikakken bayani.

Tinubu zai kara albashi

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya shirya kara mafi karancin albashi a Najeriya don rage radadi.

Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur a kasar da shugaban ya yi a watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel