Davido ya kashe Naira miliyan 240, ya sayo motar su wane-da-wane, Rolls Royce 2021

Davido ya kashe Naira miliyan 240, ya sayo motar su wane-da-wane, Rolls Royce 2021

  • Sabuwar motar shahararriyar mawakin nan, Davido da kowa ya ke sa ran gani ta shigo hannunsa
  • Tauraron ya sayo motar Rolls Royce Cullinan daga kasar waje a kan sama da Naira miliyan 200
  • Lauyan mawakin, Bobo Ajudua ya bayyana wannan da ya nuna hotonta a shafinsa na Instagram

Lagos - A yau ne mu ke samun labari cewa motar Rolls Royce Cullinan ta shekarar bana da babban mawakin nan, Davido ya saya ta shigo Najeriya.

Da alamun dai David Adedeji Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya shiryawa bikin kirismeti da na murnar sabuwar shekara ta 2022 da za a shiga da kyau.

A watan Mayun wannan shekarar shaharren mawakin ya rikita dandalin sada zumunta da hotunan wannan mota da ta ci masa sama da Naira miliyan 200.

Kara karanta wannan

Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa

A wancan lokaci, mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu da Davido yace bai da kudin da zai biya domin ayi masa dakon wannan motar har ta iso gidansa.

Bobo Ajudua, wanda shi ne lauyan mawakin, ya fito da hotunan wannan mota a zauren Instastory.

Rolls Royce 2021
Motar Rolls Royce Cullinan Hoto: @davido/@prince_ii Daga: Instagram
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya wallafa hoton motar, Ajuda yace:

“Wannan Disambar sai yadda ta kasance.”

Kamar yadda Legit.ng ta samu labari a ranar Juma’a da yamma, Bobo Ajudua yad aura hoton wannan mota tare da sauran motocin Davido a garejinsa.

Gossip Mill TV sun wallafa hoton da Ajudua ya daura a Instagram, inda yanzu mutane da-dama su ka ziyarci shafin domin cirewa kansu kwarkwatar ido.

Mawaki kuma ‘dan wasan kwaikwayon yana cikin taurarin da su ke hawa motocin alfarama masu ‘dan karen tsada a cikin tserensa a fadin nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

A halin yanzu mutane na ta tofa albarkacin bakinsu a Instagram, ana yabon yadda mawakin ya shigo da motar ba tare da ya taba kudin da aka tara masa ba.

Davido ya rabawa mabukata kudi

A kwanakin baya aka ji cewa David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya bada kyautar kudi har Naira miliyan 250 ga gidajen marayu a fadin kasar nan.

Davido ya tara Naira miliyan 200 ne bayan ya nemi duk masoyansa su tattara masa gudumuwa domin ya yi bikin cika shekara 29, daga nan sai ya kara da N50m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel