Hotunan katafaren gidan da hamshakin mawaki Don Jazzy ya tamfatsa
- Babban mawaki don Jazzy ya bar kafafen sada zumunta cike da mamaki a kan sabon gidansa
- Dan kasuwan ya wallafa hotunan katafaren gidansa wanda yasa jama'a suka dinga tsokaci
- Hatta mahaifinsa, Mavin Grandpa ya je kafar Instagram inda ya taya hamshakin dan sa murna
Babu shakka babban mawaki Don Jazzy ya shiga farin ciki tare da annashuwa bayan sanarwar da ya bada tare da hotunan katafaren gidan da ya tamfatsa a jihar Legas.
Shugaban Mavin ya wallafa hotunan sabon gidansa wanda ya gigita mabiyansa da masoyansa.
A wallafarsa, Don Jazzy cike da alfahari ya sanar da cewa ya samu kari a kadarorinsa. Don Jazzy ya tsaya a gaban katafaren gidansa wanda ya tsayu cike da haske.
KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Hadimin Ganduje yace Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus
Jim kadan bayan wallafa hotunan gidan, jama'a mabiyansa da masoyansa sun zaburo suka dinga masa fatan alheri da Allah sam barka.
KU KARANTA: Hotunan miyagun makaman da Zikwi tare da yaransa 2 suka mika ga Matawalle
A wani labari na daban, kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata.
A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin harin da 'yan ta'adda suka kai, ganau suka tabbatar. Wasu mutane 50 sun samu miyagun raunika kamar yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar.
"Ina matukar farin ciki da wannan nasarar da mayakanmu suka samu," Shekau ya sanar a wani bidiyo da Channels TV ta gani.
Ya kara da musanta cewa sojojin Najeriya sun kwace gonarsa inda yayi tunkaho da cewa yayi nasarar kafa daular Musulunci.
"Kada ka kira kanka Musulmi saboda kana sallah kuma kana bada zakka. In har ka rungumi al'adun turawan yamma baka cikinmu. Ba za mu taba zama wuri daya ba har sai ka mika wuya ga Allah," yace.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng