Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa

Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa

  • Masu bibiyar fina-finan Hausa ba su gane wasu fuskokin da suke gani, wasu gani suke yi kamar kimiyya ce wacce ke nuna fuskar mutum daya a matsayin ‘yan biyu
  • Kamar yadda tagwayen mawakan kudu, P-Square suka samu daukaka a Najeriya, yanzu Tagwayen Asali wadanda duk mawaka ne kuma hausawa sun fara haskawa
  • Tagwayen sun kasance masu sanya sutturu iri daya kuma duk inda ka ga daya za ka ga dayan sannan ko da suka tashi aure, tagwaye suka aura masu tsananin kama

Masu bibiyar fina-finan Hausa su kan ga tagwaye a matsayin salo na fasaha wacce ta ke nuna fuskar mutum daya sau biyu, amma a wannan karon ba haka ba ne.

Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa
Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa. Hoto daga @tagwayen_asali
Asali: Instagram

Tagwayen Asali

Kamar yadda kudu su ke da mawaka tagwaye, P-Square, a bangaren Hausawa kuwaa an samu wasu wadanda yanzu haka fitilar su ke haskawa.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

Sun kasance masu sa sutturu iri daya kuma duk inda ka ga daya za ka ga dayan.

Haifaffun ‘yan Kano ne, daya ya karanta fannin turanci yayin da dayan ya yi karatun Public Administration.

Sun samu daukaka don ana ta haska su a shirye-shirye daban-daban inda suke yin wakokin su.

Har aure da Tagwayen Asalin za su yi sai da suka nemi tagwaye irin su.

Sun fara waka a shekarar 2003 kuma basu da dade da yin aure ba wanda auren na su ya dauki hankali sosai.

Hassana da Hussaina Musa wadanda ake kira tagwayen Kannywood

Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa
Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Hussana da Hussaina Musa su ne tagwayen da Kannywood suka fi alfahari da su. Duk asali ‘yan Kano ne kuma sun yi karatun su a cikin jihar inda Hussaina ta yi karatu a fannin lafiya kuma yanzu haka tana aiki da ma’aikatar muhalli, yayin da Hassana ta karanta fannin ilimin addinin musulunci a kwalejin Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

‘Yan biyun su na cikin tagwayen da suke burge mutane da dama saboda tsananin kamannin su da juna.

Sun shahara kwarai a Kannywood don ana kiran su da Tagwayen Kannywood. Sun yi fina-finai kamar Mairon Kauye da Mizani.

Sun yi fina-finai fiye da 30 kuma sun nuna kwarewa rsu kwarai a duk fina-finan da su ka yi.

Hassana da Hussaina Yusuf na Dadin Kowa

Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa
Hotunan tagwaye 3 da ke nishadantar da masu kallo a masana'antar fina-finan Hausa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Hassana da Hussaina shekarun su 27 kuma kamanin su daya. Haifaffun Maiduguri ne a jihar Borno. Sun shiga masana’antar Kannywood kusan shekaru 7 da suka shude.

Sun yi karatun su na sakandare a Borno inda suka zarce Jami’ar Maiduguri inda su ka yi Diploma a fannin Social Work kafin su koma Kano su shiga masana’antar Kannywood.

Sun bayyana a fina-finai kamar Sai Na yi Kudi, Talatu Numba Daya, Kudiri da sauran su kuma sun shahara ne a shirin fim din Dadin Kowa na Arewa 24.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Asali: Legit.ng

Online view pixel