Mawaka 3 da suka fi kowa kudi a Najeriya

Mawaka 3 da suka fi kowa kudi a Najeriya

– Duk Mawakan Najeriya babu wadanda su ka kai P-Square kudi

– Ba a bar su Don Jazzy da D-Banji da su 2-Face a baya ba

– Davido da Wizkid su na cikin sahun masu kudi

Kamar yadda aka saba a kowace shekarar Mujallar Forbes kan fito da sunayen wadanda su ka fi kowa a arziki.

Wannan karo mun zakulo wadanda su ka fi kowa kudi a Najeriya cikin Mawaka.

Ko wanene a kan gaba?

Mawaka 3 da suka fi kowa kudi a Najeriya
P-Square

KU KARANTA: Matsaloli 8 na 'Yan Najeriya

1. P-Square

Ko dama can tagwaye ne kuma tare su ka saba wakokin su. Duk Najeriya dai babu wadanda su ka taka arzikin P-Square wadanda sun ba Naira Biliyan 15 baya.

2. Don-Jazzy

Wannan Gwarzon kan shiryawa Jama’a waka, daga cikin irin wadannan akwai su Korede Bello, Iyanya, Tiwa Savage da sauran su. Ya mallaki sama da Naira Biliyan 6.5.

3. D’Banj

Babban Mawakin nan da aka sani da ‘Koko Master’ ya ba Naira Biliyan 5 baya. Kwararren Mawaki ne kuma ya san yadda yake nemo kudin sa.

Mawaka 3 da suka fi kowa kudi a Najeriya
D-Banj da kuma 2-Face a wani shiri

KU KARANTA: Mahaifiyar da ta fi kowa tsufa a Najeriya

Akwai irin su 2-Face, Davido, Wizkid, Timaya da su Banky-W wadanda su ma sun samu alheri da waka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Matashi ya zama shugaban kasa a Faransa

Asali: Legit.ng

Online view pixel