Ana Cikin Tsadar Rayuwa Shahararren Mawaki a Najeriya Zai Raba N300m Ga Gidajen Marayu

Ana Cikin Tsadar Rayuwa Shahararren Mawaki a Najeriya Zai Raba N300m Ga Gidajen Marayu

  • Davido ya sanar da ware zunzurutun kuɗi har naira miliyan 300 domin gidajen marayu dake faɗin ƙasar nan
  • Shugaban na kamfanin waƙa na DMW ya yi wannan sanarwar mai ban sha'awa ga jama'a ta kafafen sada zumunta a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu
  • Davido ya bayyana cewa alƙawarin da ya ɗauka na miliyoyin na daga cikin gudunmawar da yake ba Najeriya duk shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Fitaccen mawaƙin nan na Najeriya, David Adeleke Davido ya zama abun magana a shafukan sada zumunta game da yadda yake nuna soyayya ga mabuƙata da marasa galihu, musamman a cikin tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya.

Davido, wanda cikin ƴan kwanakin nan ya zama abun magana kan kasancewarsa a wurin bikin ranar haihuwar Memphis Depay, inda ya karɓi agogon Rolex, ya bayyana cewa zai bayar da kuɗi Naira miliyan 300.

Kara karanta wannan

'Yan kwadago sun jero sabbin sharuɗda ga Gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa, bayanai sun fito

Davido zai ba marayu kyautar N300m
Davido zai ba gidajen marayu gudunmawar N300m Hoto: @davido
Asali: Instagram

Cikakkun bayanai kan gudunmawar N300m da Davido ya bayar

Shugaban kamfanin na DMW, wanda ya aka yi ta magana a kansa a shekarar 2021 bayan tara sama da Naira miliyan 200 ga gidajen marayu a lokacin zagayowar ranar haihuwarsa, ya bayyana cewa Naira miliyan 300 ya yi alƙawari ne ga gidajen marayu a faɗin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Davido ya kuma ce gudunmawar wani bangare ne na gudunmawar da yake bayarwa duk shekara, inda ya ƙara da cewa za a bayyana cikakken bayani kan yadda za a rabar da kuɗaɗen daga ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

Mawaƙin ya rubuta cewa:

"Ni da gidauniyata mun yi alkawarin bayar da Naira miliyan 300 ga gidajen marayu da ke faɗin Najeriya… a matsayin gudunmawar da zan bayar a kowace shekara ga al'ummar ƙasa. Gobe za a bayyana yadda za a raba kuɗaɗen."

Kara karanta wannan

Ganduje ya samu matsala a APC yayin da tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar, ya fadi dalili

Ƴan Najeriya sun mayar da martani kan alkawarin da Davido

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da ƴan Najeriya suka yi, inda da yawa suka yabawa mawaƙin.

Ga wasu daga ciki nan ƙasa:

adesope_shopsydoo:

"David yaron kirki."

nachiblessingsunday:

"Na zama maraya oooo."

Rankingofficial:

"Ubangiji na ƙaunar duniya sai ya ba mu Davido."

vivaglow_beauty:

"Baba ya bar gidan marayu ya shiga titi.. jama'a suna jin yunwa.. Wasu ko'odinetocin wasu gidajen marayun ba za su yi amfani da kuɗin a kan yaran ba.. sai dai su arzuta kan su.. Ka ba talakan da a halin yanzu ma ba ya iya siyan abinci ko sau ɗaya @davido."

Davido Ya Faɗi Matsalar Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shaharrren mawaƙin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya faɗi babbar matsalar Najeriya.

Mawaƙin wanda ya yi suna a Najeriya da ƙasashen waje ya bayyan cewa ƙudi sune suka haifar da matsalar da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel