Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

  • David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu fiye da Naira miliyan 120 daga hannun masoyansa
  • Shahararren mawakin Najeriyar ya nemi a turo masa kudi domin ya gane masoyansa na hakika
  • Davido wanda zai cika shekara 28 a ranar Lahadin nan yace yana neman kudin shigo da Rolls Royce

Nigeria - Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu miliyoyin kudi daga jama’a bayan da ya nemi a tara masa kudi.

A lokacin da Legit.ng Hausa ta ke tattara wannan rahoto a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, 2021, sama da Naira miliyan 120 ne suka shiga asusun Davido.

Hakan na zuwa ne bayan mawakin ya yi magana a shafinsa na Instagram, inda yake tsokanar masoyansa da cewa su taimakawa sana’arsa da Naira miliyan daya.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya a waje: Yadda dan Najeriya ya hargitsa zaman lafiyar kantin sayayya a kan kudi

“Ana taimakon wanda yake taimako, ko bah aka ba ne? Nima na ci sa’a ne a shekarun nan ta hanyar taimakon wasu. Saboda haka ina son sanin su wanene ainihin abokai na. Duk abokai na su tura mani Naira miliyan daya.”
“Idan ba ka turo maki na ka ba, ba mu tare da kai.” – Davido.

Su wanene suka tarawa Davido kudi?

Domin ya nuna da gaske yake yi, Adeleke ya nuna hujjar da ke nuna an fara turo masa kudi a asusunsa. Kafin a ce mene, sai kudi suka rika shigowa ta ko ina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch tace wadanda suka aikawa mawakin kudi sun hada da wani ‘dan majalisa na jihar Oyo, Akin Alabi, da babban ‘dan kasuwar nan, Emeka Okonkwo.

Davido
Davido yana wasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa mawaka da sauran ‘yan wasa irinsu Mr Eazy, Teni, Chike, Zlatan, Adekunle Gold, Perruzi, da Ikorodu Bois duk sun aiko gudumuwa.

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Manyan Attajirai irinsu Obi Cubana da Femi Otedola sun aiko masa kudin da suka girgiza shi.

MI Abaga yana so ya yi waka da Davido

Kamar yadda Daily Post ta fitar da rahoto, fitaccen mawakin nan, MI Abaga ya aiko da na shi Naira miliyan dayan, kuma ya roki Davido su hadu, su yi waka tare.

Davido wanda zai cika shekara 28 a karshen makon nan yace yana bukatar kudi domin ya samu kudin da zai sallami hukuma, ya dauko motar da ya sayo daga waje.

A halin yanzu dai kudin kara yawa suke ta yi, Davido da yace yana neman Naira miliyan 100, ya dawo yana cewa yanzu ya na harin a turo masa Naira miliyan 200 ne.

Sojojin sun yi ta'adi a #LekkiGate

Kwamitin da ya yi bincike a kan rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS yace shakka babu Sojoji sun yi wa matasa kisan gilla a kofar shiga Lekki a Legas.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

Rahoton binciken ya nuna cewa bayan sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zangar lumuna, sun boye gawawwaki, kuma sun hana a kai mutane masu rauni asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel