"A Shirye Na Ke Na Yi Wuff Da Babban Kwamandan Hisbah Na Jihar Kano", Hafsat Fagge

"A Shirye Na Ke Na Yi Wuff Da Babban Kwamandan Hisbah Na Jihar Kano", Hafsat Fagge

  • Shahararriyar mai rawar TikTok a jihar Kano, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta yi wuff da babban kwamandan Hisbah na jihar
  • Hafsat Fagge ta bayyana cewa idan dai har shugaban na Hisbah yana son ta da aure, to za ta amince ta aure shi
  • Ta kuma bayyana cewa yanzu ta tuba ta daina rawa a TikTok inda ta rungumi hanyar neman ilmin addinin musulunci

Jihar Kano - Shahararriyar ƴar TikTok a jihar Kano, Hafsat Fagge, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta amshi tayin aure daga wajen babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Hafsat ta bayyana hakan ne a wani bidiyon wata hira da aka yi da ita wacce ta sanya shafinta.

Kara karanta wannan

A sharar titi: Yadda wata mata ke hada sama da N860k a sana'ar shara

Hafsat Fagge ta tuba da rawa a TikTok
Hafsat Fagge tana son ta yi wuff da Sheikh Ibn Sinah Hoto: Bashir Sani Abubakar
Asali: Facebook

Hafsat Fagge wacce aka fi sani da Hafsat Baby, wacce hukumar Hisbah ta gayyace ta kwanan nan kan bidiyoyin rawarta a TikTok, ta bayyana cewa ta goge dukkanin bidiyoyin daga shafinta.

Ta tuba da yin rawa a TikTok

Ta kuma ƙara da cewa ta daina yin rawa da ɗorawa a shafinta na TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

"Hisbah sun kira ni a waya kan bidiyon rawar da na ke yi tare da Lawancy, kuma na yi musu alƙawarin daina yin rawa. Na kuma goge dukkanin bidiyoyin rawar da suka tayar da ƙura."

Da aka tambaye ta ko wane shiri ta ke da shi a nan gaba, Hafsat ta bayyana cewa ta yarda da so sannan duk wanda ya ke son ta, to ya zo ƙofa a buɗe ta ke.

Ta ƙara da cewa a shirye ta ke ta amshi tayin aure daga babban kwamandan na Hisbah, idan har ya nuna yana son ya yi wuff da ita, cewar rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

"Sai Wasa Da Maza a Jeji": Mahaifiya Ta Fallasa Sakamakon 'Yarta Budurwa, Kalaman Malamarsu Ya Jawo Muhawara

"Idan har babban kwamandan Hisbah yana son ya aure ni a matsayin matarsa, zan yarda da hakan cikin farin ciki. Ina so yanzu in mayar da hankali kan karantun addinin musulunci domin na samu ilmi sosai."

Boka Ya Gurfana Gaban Kotu Kan Yi Wa Jarumar Kannywood Sata

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun gurfanar da wani boka a gaban kotu kan zargin yi wa jarumar Kannywood, Fati Muhammad, sata.

Ana zargin bokan ne dai da haɗa baki da ɗan uwan jarumar wajen sace mata motar hawa bayan sun ba ta wani abu da ya gusar mata da hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel