"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

  • Wani matashi da ya shiga ɗimuwa bayan rabuwa da masoyiyar sa, ya tura mata wani saƙo domin ganin ta dawo gare shi
  • Ya bayyana cewa shi mummuna ne kuma ba kowan kowa ba idan babu ita, furucin da ya fusata samari da dama a soshiyal midiya
  • Mutane da dama da suka kalli hirar sa da budurwar, sun yi Allah wadai kan yadda ya susutar da kan sa, wasu ƙalilan sun goya masa baya

Wani matashi ya fusata mutane kan wani saƙo da ya turawa tsohuwar budurwarsa, domin ganin ta dawo sun ci gaba da soyayya.

Wani mai amfani sunan @SooSlept_On, a manhajar Twitter, ya yi masa kaca-kaca kan kalmomin da ya yi amfani da su, inda ya ce ya fara zaucewa.

Matashi ya roki tsohuwar budurwarsa ta yafe masa
Matashin ya roki budurwar sa yafiya Hoto: Mireya Acierta, Tim Roberts, Twitter/@SooSlept_On
Asali: Getty Images

@SooSlept_On ya bayyana cewa ko da wasa ba zai taɓa gayawa mace waɗannan kalmomin ba.

A cikin hirar ta su da aka fitar, matashin mai suna Freddie ya gayawa tsohuwar budurwar ta sa cewa shi ba kowan kowa bane idan babu ita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya nanata cewa ya shiga garari a rashin ta, sannan ya sha alwashin sanya ta farin ciki inda ya ƙara da cewa yana matuƙar son ta.

Matashin ya ƙarƙare neman afuwar da yake ta hanyar yin amfani da wasu alamomi guda biyu. Sai dai, budurwar ba ta gamsu da ƙoƙarin da matashin ya yi ba, inda ta mayar masa da martanin cewa bai yi ƙoƙari ba ta hanyar amfani da wasu alamomi.

Kaɗan daga cikin abinda ƴan soshiyal midiya suka ce:

@DosMasPorFavor ya rubuta:

"Ina jin daɗin yadda kowa ya ke nuna shi gwarzo ne, kafin wani ya samu kan shi cikin irin wannan halin, daga nan sai mu dawo hayyacin mu."

@Iam_Ambros ya rubuta:

"Toh yanzu duk samarin nan kuna so ku ce ba ku taɓa fayyace wa budurwar su halin da zukatan su ke ciki ba."

@babywavecap ya rubuta:

"Na faɗi abubuwa sosai lokacin da na samu tawa matsalar, amma ban taɓa faɗin wanda suka kai haka ba."

@dontmindlearnin ya rubuta:

"Ni ma irin wannan tunanin na yi lokacin da na karanta, amma saboda gaskiya ni ma na yi wasu abubuwan da bai yi ba. Haka abubuwan su ke."

Dirarriyar Budurwa Ta Yaudari Mahaifinta a Matsayin Budurwarsa, Ya Tura Mata Kudade

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda wata budurwa ta yaudari mahaifinta ya tura mata maƙudan kuɗaɗe.

Budurwar ta bayyana cewa, ta yaudari mahaifinta ne inda ya yi tunanin cewa ya samu budurwa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel